Shugaban Jam’iyya da ya yi Murabus ya Hango Makomar Kwankwaso, NNPP a 2023
- Tsohon shugaban NNPP a jihar Kaduna, Ben Kure ya yi karin-haske a kan barin jam’iyyar da ya yi
- Ben Kure ya ce shi da kan shi ya rubuta takardar ajiye aiki saboda sabani da ‘dan takaran Gwamna
- Yayin da zabe ya gabato, ‘dan siyasar ya na ganin jam’iyyar NNPP tana cikin matsala a Kaduna
Kaduna - Ben Kure tsohon shugaban NNPP ne na reshen jihar Kaduna, a hirar da aka yi da shi, ya yi bayanin abin da ya kai shi ga barin jam’iyyar.
Ben Kure ya shaidawa Daily Trust cewa shi da kan shi ya rubuta wasika, ya sanar da uwar jam’iyya cewa ya sauka daga shugabancin NNPP a Kaduna.
Wannan ya sabawa rahotannin da ke cewa ‘yan majalisar zartarwa na jam’iyyar NNPP ne suka hadu, suka tunbuke Kure daga kujerar da yake kai.
"Ba sauke ni aka yi ba; na rubuta murabus ne zuwa ga sakatariyar jam’iyya a ranar 5 ga watan Disamba 2022, amma aka roki in zauna domin a sasanta cikin ruwan sanyi.
‘Dan takaran Gwamna, Suleiman Othman Hunkuyi da wasu katsalandan da aka rika yi mani ba a kan ka’ida ba, suka hana ni gudanar da aiki na domin cigaban jam’iyya."
- Ben Kure
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kure yana aiki da APC?
A kan zargin da ake yi masa na yi wa jam’iyyar APC mai mulki aiki, Kure ya musanya hakan.
"Wadannan soki-burutsu ne kurum. idan suna da hujja, su fito da ita fili. Tun da tsohon mai gidana, Nasir El-Rufai ya kore ni Mayun 2021, ban tunani na sake ganinsa."
- Ben Kure
Game da kokarin da uwar jam’iyya tayi wajen ganin an sasanta rigimar cikin gidan, Kure ya ce ta ankarar da shugabannin NNPP na kasa a Abuja.
“Maganar gaskiya na fadakar da ‘dan takaran shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso – mutumin da nake kauna kuma nake girmamawa sosai.
Saboda girmama shi da nake yi ne na dade haka a NNPP; domin da farko nayi tunanin abubuwa za su gyaru, sai ya had ani da shugaban jam’iyya.
Amma abubuwa ba su canza zani ba domin Kwankwaso da shugaban jam’iyya na kasa sun yarda da shi, sun ba shi damar ya kafa shugabanni.
- Ben Kure
A karshen hirar da aka yi da shi, an rahoto Kure yana cewa ba a labarin NNPP a Kaduna, amma ya ce a zaben kasa, Rabiu Kwankwaso zai yi tasiri.
‘Dan siyasar yana ganin Kwankwaso yana cikin ‘yan takaran shugaban kasan da suka fi dacewa, ya ce babu dalilin hada shi da abokan gaban na sa.
Rigimar PDP a Ekiti
Kun ji labari cewa rikicin PDP ya yi tasiri a jihar Ekiti, wadanda Aminu Waziri Tambuwal ya zaba a kwamitin kamfe sun ki amincewa su karbi aikin.
‘Yan takaran Sanatoci da na majalisar tarayya sun rubuta wasika, suka bayyana abin da zai hana su yi wa Atiku Abubakar kamfe a dalilin sabanin gida.
Asali: Legit.ng