Bauchi: Tsohon Gwamnan APC Ya Yi Watsi da Jam’iyyarsa, Yana Goyon Bayan PDP

Bauchi: Tsohon Gwamnan APC Ya Yi Watsi da Jam’iyyarsa, Yana Goyon Bayan PDP

  • Tsohon Gwamnan jihar Bauchi ya nuna yana goyon bayan Gwamnatin Bala Abdulkadir Mohammed
  • Mohammed A. Abubakar ya yabawa Sanata Bala Abdulkadir Mohammed a wajen wani biki da aka shirya
  • Magoya bayan ‘dan takaran Gwamnan APC na jihar Bauchi, Sidique Abubakar ba su ji dadin lamarin ba

Bauchi - Tsohon Gwamnan jihar Bauchi, Mohammed A. Abubakar yana goyon bayan Bala Abdulkadir Mohammed ne a zaben Gwamna da za ayi.

Premium Times ta ce goyon bayan da Mohammed A. Abubakar ya ba Gwamna mai-ci wanda yana PDP, ya hada shi fada da ‘ya ‘yan jam’iyyarsa ta APC.

Wasu ‘yan APC mai adawa a jihar Bauchi sun bada shawarar a kori Mohammed A. Abubakar daga jam’iyya duk da matsayinsa na wanda ya yi Gwamna.

A wata liyafa da aka shirya domin karrama tsohon Gwamnan bayan ya kai matsayin SAN a gidan shari’a, sai aka ji ya yi wa Bala Mohammed mubaya’a.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Yi Irin Na Tinubu, Ya Tafka Katuwar Katobara Gaban Jama’a Wajen Kamfe

Mubaya’ar M. A Abubakar

Da yake jawabi, babban Lauyan ya ce ya yi mamakin ganin Mai girma Gwamnan Bauchi ya halarci bikin da aka shirya saboda taya shi murna zama SAN.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abubakar yake cewa haka ya kamata a rika yin siyasa ba tare da gaba ba, ‘dan siyasar yake cewa yau PDP take mulkin Bauchi, kafin nan kuwa APC ce.

Bauchi
Shugaban Najeriya, Buhari a Bauchi Hoto: www.sunnewsonline.com
Asali: UGC

“Yau PDP take mulki a jihar Bauchi, jiya jam’iyyar APC ce. Wani yana jam’iyyar PDP a yau, zai iya komawa APC washegari.
Tun da burin da muke da shi, shi ne cigaban jihar, ina goyon bayan cigaban da ya kawo. Ina farin ciki cewa Bauchi tana cigaba.
Na san za a fadi abubuwa da yawa a game da taron daren nan, amma mafi muhimmanci shi ne kanina ya ba ‘yan siyasa aiki.

Kara karanta wannan

Sanatan PDP Ya Ba Buhari Uzuri, Ya Fadi Inda Aka Samu Matsala a Gwamnatin APC

Ina rokon Allah ya cigaba da yi masa (Bala Mohammed) jagoranci wajen tafiyar da harkar jihar nan.”

- Mohammed A. Abubakar

Siyasar Bauchi ta dauki zafi

Abin da ya batawa magoya bayan APC na jihar Bauchi shi ne, ‘dan takaran Gwamna, Sidique Abubakar ya gayyaci Abubakar wajen liyafa, ya ki zuwa.

An rahoto Kakakin kwamitin neman zaben Gwamnan APC a Bauchi, Salisu Ahmad – Barau, yana cewa tsohon gwamnan ya ci amanar Sidique Abubakar.

Tsakanin 2015 da 2019, kuna da labari M. A Abubakar ne Gwamnan Bauchi, a zaben da ya nemi tazarce, ya sha kashi a hannun Sanata Bala Mohammed da PDP.

Tsohon Gwamnan yana zargin cewa wasu jagororin APC suka yaudare shi a zaben 2019, suka marawa tsohon Ministan birnin tarayyan, har ya iya lashe zabe.

An kama 'danuwan gwamna

An samu rahoto Lauyan Hukumar EFCC zai yi shari'a a kotun tarayya da wani wanda yaro ne a wajen Gwamnan jihar Kogi tare da wasu mutane biyu a Abuja.

Kara karanta wannan

Shugaban APC na Kasa, Sanata Adamu, Ya Bayyana Magajin Buhari

EFCC tana zargin Ali Bello, Dauda Sulaiman da Abdulsalami Hudu da laifin satar N10, 270,556,800 daga baitul-mali, sannan aka juya biliyoyin a wajen ‘yan canji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng