Kotu Ta Kori Karar Tsohon Ministan Buhari da Ya Nemi a Hana Atiku da Tinubu Takara a 2023
- Kotu ta yi da watsi da karar tsohon karamin ministan Ilimi, wanda ya nemi ta kori Atiki da Tinubu daga takara a 2023
- Chukwuemeka Nwajiuba tare da wata kungiya mai zaman kanta sun nemi a maye gurbin Tinubu da tsohom Ministan
- Daga karshe, Kotun ta soki kungiyar RAI bisa wuce gona da iri daga manufar da ta yi rijista, kana ta rushe ta baki ɗaya
Abuja - Babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja ta yi fatali da ƙarar da tsohon ƙaramin Ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, tare da wata kungiyar kare hakkin ɗan adam RAI suka shigar kan manyan 'yan takara biyu.
The Nation da rahoto cewa tsohon Ministan tare da kungiyar RAI mai zaman kanta sun kai ƙarar Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban kasa a PDP da takwaransa na APC, Bola Tinubu gaban Kotu.
2023: "Ka Ci Zaɓe Ka Ci Zabe" Yadda Dubun Dubatar Magoya Baya Suka Yi Maraba da Tinubu a Jihar Arewa
A ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/942/2022, Nwajiuba da RAI sun roƙi Kotun ta rushe zabukan fidda gwanin da suka samar da Atiku da Tinubu a matsayin 'yan takarar shugaban kasa na PDP da APC.
Haka zalika sun roki Kotun ta maye gurbin Bola Tinubu na APC da tsohon Ministan, wanda yace ya fafata a zaben fidda ɗan takarar APC kuma bai samu ko kuri'a ɗaya ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa sun jera waɗanda suke kara da suka haɗa da, APC, PDP, Tinubu, Atiku, Antoni Janar na tarayya da kuma hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC).
Hukuncin da Kotu ta yanke yau Alhamis
Da yake yanke hukunci ranar Alhamis, Mai shari'a Inyang Ekwo, ya musanta masu ƙara da cewa basu da hurumin shari'a na shigar da ƙara gaban Kotu kan batun.
Yan Najeriya Sun Samu Sabon Sumfurin Shugaba Buhari, Doguwa Ya Jaddada Wanda Ya Dace da Mulki a 2023
Alkalin, wanda ya ayyana cewa ko kaɗan ƙarar ba ta dace ba, ya kuma yi Allah wadai da tsoma hannun RAI, ƙungiya mai zaman kanta a harkokin da suka shafi siyasa.
Yace tsoma hannun RAI a Kes ɗin siyasa ta tsallake manufofin da ta kafu a kai wanda ta yi rijista da su a sashi na F na kundin dokokin kamfanoni CAMA a hukumar CAC.
"A ƙasar nan ne kawai zaka ga ƙungiyoyin da suka yi rijista kan manufa daban sun shiga siyasa," Injji Alkalin, kamar yadda Tribune ta ruwaito.
Daga nan kuma ya zarce kan yanke hukuncin rushe RAI sannan ya umarci CAC fa kwace iko da ƙungiyar kuma ta bi tanadin doka wurin tabbatar da umarnin Kotu.
A wani labarin kuma Kotun Ɗaukaka kara ta sauya hukuncin babbar Kotu, tace 'yan takarar APC a Ribas su shiga a fafata da su a zaɓen 2023
Tun farko dai Alkalin babbar Kotun tarayya ta rushe baki ɗaya zabukan fidda gwanin APC na jihar Ribas, tace sun tanƙwara doka wurin zaɓo Deleget.
Asali: Legit.ng