An Nemi Bola Tinubu An Rasa Ana Tsakiyar Kamfe, APC Ta fito Tayi Karin Haske

An Nemi Bola Tinubu An Rasa Ana Tsakiyar Kamfe, APC Ta fito Tayi Karin Haske

  • Asiwaju Bola Tinubu bai nan lokacin da aka tashi taron yakin neman zaben APC a garin Minna
  • Kafin taron ya kammala, ‘dan takaran shugaban kasar ya bar filin kasuwar baje-koli da ke Neja
  • Bayo Onanuga ya fitar da jawabi, ya na musanya cewa rashin lafiya ta sa aka fita da Tinubu

Niger - Ba wani abin tashi hankali ya jawo Asiwaju Bola Tinubu ya bar filin kamfe a lokacin da ba a tashi ba, kamar yadda wasu suke kokarin nunawa.

Punch ta ce Darektan yada labarai da hulda da jama’a na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a APC ya fitar da jawabi a kan abin ya faru yau.

A ranar Larabar nan, Bola Tinubu da shugabannin APC suka je Minna, jihar Neja domin kamfe. Hakan na zuwa ne bayan gangamin da aka yi a Kaduna.

Kara karanta wannan

'Yan PDP Sun Shiga Zulumi, An yi Taron Gangamin Kamfen, Fili a Bushe a Wata Jahar Arewa

A jawabin Bayo Onanuga, ya musanya rade-radin cewa an dauke ‘dan takaran na jam’iyyar APC daga taronsu da aka yi a Minna ne saboda rashin lafiya.

An ga mutane iya mutane - APC PCC

Onanuga yake cewa saboda dinbin mutanen da suka fito ganin ‘dan takaran shugaban kasar a jihar Neja, sai dai ya yi masu jawabinsa a gurguje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Onanuga, a tarihi ba a taba ganin farfajiyar kasuwar Duniya da ke binrin Minna ta cika makil da dinbin mutane kamar yadda aka gani yau ba.

Tinubu
Bola Tinubu yana kamfe a Bayelsa Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Jawabin darektan yada labaran ya fito a shafin yanar gizon ‘dan takaran na jam’iyyar APC mai mulki da abokin takararsa a zaben 2023, Kashim Shettima.

Jawabin Bayo Onanuga

“Akasin jita-jitar da ake yi cewa rashin lafiya ta sa aka dauke Tinubu daga taro, Tinubu ya hanzarta ne domin halartar wasu taron ranar.

Kara karanta wannan

Zulum ya Kaddamar da Yakin Neman Zabensa na 2023 a Borno

(Tinubu) ya jinjinawa magoya bayan jam’iyyar da suka fito kwansu da kwarkwatarsu domin halartar bikin fara yakin zaben shugabancin kasa."

- Bayo Onanuga

Meya faru bayan gangamin?

Jawabin ya ce bayan taron, Tinubu ya kaddamar da ofishin yakin neman zabensa da shugaban gidan jaridar Blueprint, Mohammed Malagi ya ba shi kyauta.

‘Dan takaran ya samu lokaci ya kai ziyarar ban girma zuwa fadar Sarkin Minna, a karshe kuma ya halarci liyafar da Gwamna Abubakar Sani Bello ya shirya.

Kwabar Atiku a Filato

Da aka je yawon yakin neman zaben PDP, an ji labari Atiku Abubakar mai shekara 76 ya yi irin subul da bakan da Bola Tinubu ya yi da aka je a garin Jos.

An ji Atiku a bidiyo yana kira ga Josawa: "Domin darajar Ubangiji da darajar wannan wuri, ku tabbatar kun zabi A…(Ina nufin), PDP a wannan karo. PDP!!!

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng