2023: Nagode Allah Da Ba Nine Abokin Takarar Tinubu Ba, In Ji Dogara

2023: Nagode Allah Da Ba Nine Abokin Takarar Tinubu Ba, In Ji Dogara

  • Honourable Yakubu Dogara, na ci gaba da nuna adawarsa ga tikitin Musulmi da Musulmi a zaben shugaban kasa
  • Tsohon kakakin majalisar wakilai ya ce tikitin addini guda na da matukar hatsari kuma yana iya haddasa rikici a Najeriya
  • Dogara ya kuma yi watsi da batun cewa yana adawa da tikitin Musulmi da Musulmi na APC ne saboda ba a zabe shi a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasar jam'iyyar ba

Bauchi - Tsohon kakakin majalisar wakilai, Honourable Yakubu Dogara, ya bayyana cewa yana farin ciki da ba shine abokin takarar Bola Ahmed Tinubu ba a babban zaben shugaban kasa na 2023.

Jaridar Nigerian Tribune ta rahoto cewa Dogara ya yi furucin ne yayin wata hira da manema labarai a Bauchi.

Bola Tinubu
2023: Nagode Allah Da Ba Nine Abokin Takarar Tinubu Ba, In Ji Dogara Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Dogara na martani ne ga wata tambayar da ke cewa baya goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) saboda ba a zabe shi a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar mai mulki ba.

Kara karanta wannan

Yaro Mai A Bakwai a Jarabawar WAEC Ya Zauna a Gida Saboda Rashin Kudin Zuwa Jami'a

Kalamansa na cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ina ganin wannan shine kawai abun da za a iya fadi idan ana son kawar da hankalin jama'a daga zahirin gaskiya kan siyasar da ya yi watsi da kusan rabin kasar.
"Bisa fahimtata ga wannan lamari, ina matukar godiya ga Allah cewa hakan bai faru ba kuma abokai da masoya da dama sun fada mani cewa suna godiya ga Allah a kullun da bana cikin wannan tikitin wanda ya basu damar gani da sanin wanene dan takarar.
"Kun zata da yawan mutanen da ke bin Tinubu a yau makafai ne? Sun hango hatsarin amma suna duba abun da za su samu sama da ra'ayin kasar."

Masu tallata tikitin Musulmi da Musulmi suna da matukar hatsari, Dogara

Dogara ya kuma bayyana cewa ya kamata yan Najeriya su yi hankali da wadanda ke tallata tikitin Musulmi da Musulmi.

Kara karanta wannan

Kowa ya huta: Atiku ya fadi yadda zai yi kungiyar ASUU idan ya gaji Buhari a zaben 2023

Dogara ya kara da cewa:

"Abun da nake kokarin jan hankali a kai shine cewa wadanda ke tallata tikitin addini daya da zaban addini daya ba wai kawai basu da hankali bane, suna da hatsari. kamar masu ingiza kiyayya a tsakanin kabilu.
"Magana ta gaskiya ita ce idan mutanen kirki kamar ku da ni bamu tashi mun hana su ba, wadanda basu da cikakken hankalin yarda da cewar za su hana mu gina al'umma wacce kanta ke hade za su yi nasara wajen lalata kasar nan da muke matukar kauna.
"Don haka ya zama wajibi mu tashi a kan wadannan muryoyi masu hatsari kuma ba wai kawai mu tashi a kansu ba, illa mu like bakinsu don dukkanmu mu kafa tarihi da gina kasar nan.
"Wannan ne dalilin da yasa ban taba goyon bayan tikitin Kirsita da Kirista ko Musulmi da Musulmi ba a kasa mai yawan addinai, kabilu da al'adu irin Najeriya."

Kara karanta wannan

Dan Ba Kara Zaben APC A 2023: Mun Zabi Buhari Wahala Ta Kusan Kashe Mu, iInji 'Yan Arewa

A gefe guda, Dogara ya kuma bukaci yan Najeriya da su dauki tsattsauran mataki don magance matsalar shugabancin kasar a 2023, jaridar Vanguard ta rahoto

Na yi iya abun da zan iya a matsayin shugaban kasar Najeriya, Buhari

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a tsawon shekaru bakwai da rabi da yayi yana mulkar Najeriya ya yi iya bakin kokarin da zai iya.

Buhari ya ce gwamnatinsa ta bayar da muhimmanci sosai wajen inganta rayuwar matasa domin sune yara manyan gobe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng