Shugaba a PDP ya Fallasa Tinubu, Kuma Yana barazanar ba Zai Zabi Atiku a 2023 ba
- Babu tabbacin cewa Legas ce asalin Asiwaju Bola Tinubu, a ra’ayin jagoran adawa a PDP, Bode George
- Duk da Tinubu ya yi Gwamna na shekara takwas a Legas, Cif Bode George bai yarda da nasabarsa ba
- George ya nuna idan ba a dinke barakar PDP ba, ba zai zabi ‘dan takaran su na shugaban kasa ba
Lagos - Jagora a jam’iyyar PDP, Bode George, ya ce ‘dan takaran shugabancin kasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ba ‘Dan jihar Legas ba ne.
An yi hira da Cif Bode George a wani shiri da ake yi a gidan talabijin Arise TV, inda ya yi magana a kan takarar Bola Tinubu da rikicin gidan PDP.
Bode George ya yi ikirarin har yanzu Tinubu bai iya gamsar da Duniya cewa shi mutumin Legas ba ne domin babu abin da ke nuna tatson shi a jihar.
‘Dan siyasar yana cikin masu bakar adawa ga tsohon Gwamnan na jihar Legas tun ba yau ba.
A Isale-Eko Tinubu ya tashi?
“Ba daga Legas Bola Tinubu ya fito ba. Ku ce ni ne na fada maku wannan. Idan ya ce a Isale-Eko ya tashi, wace makaranta ya halarta?
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A layin Evans na tashi a Legas, gida mai lamba na 35 a layin ne na kakanmu. Na halarci makarantar yanki, na biga kwallo a filin Isale-Eko.
A haka mutane su ka san ni.”
- Bode George
Rikicin jam’iyyar hamayya
A game da rigimar da ake yi a jam’iyyar PDP, George ya ce za a shawo kan matsalar ne idan har aka yi abin da ya kamata wajen samun zaman lafiya.
Punch ta rahoto tsohon mataimakin shugaban PDP na kasar yana cewa babu adalci a ce daga Arewa maso tsakiya ne ake ta fito da shugaban jam’iyyar.
Solomon Lar, Audu Ogbe, Dr Amadu Ali, da Abububakar Kawu Baraje duk daga yankin suka fito, yanzu ga shi PDP tana hannun Iyochia Ayu daga Benuwai.
Ba zai zabi Atiku ba idan...
“Kudu maso yamma ba su taba rike wannan mukami ba tun da aka kafa jam’iyyar kusan shekaru 25 da suka wuce. Menene laifinmu?
Idan kana neman mulki kasar nan, dole ka tafi da kowace kabila. Wannan ce babbar matsalar,
Kuma idan ba a magance wannan matalsar ba, ba zan zabi ‘dan takaran jam’iyyarmu ba.”
- Bode George
NNPP za ta hade da APGA?
A jiya aka samu labari Rabiu Musa Kwankwaso tare da shugabannin jam’iyyar NNPP na kasa sun hadu da ‘dan takaran APGA a zaben Shugaban Najeriya.
Har zuwa yanzu, ba mu san wainar da aka toya yayin da Farfesa Peter Umeadi ya sa labule da ‘dan takaran kujerar shugabancin kasan na NNPP a 2023.
Asali: Legit.ng