Ta Yaya Ka Tara Dukiyarka Idan Da Gaske Gidanku Talakawa Ne, Atiku Ya Kalubalanci Tinubu
- Bayan hirarsa a Landan, Atiku Abubakar ya kalubalanci Asiwaju Tinubu da ya zo ya yi bayani game da tushen arzikinsa
- Dan takarar shugaban kasa na PDP ya ce babu yadda za a yi wanda ya yi ikirarin fitowa daga gidan talakawa ya gaji tarin arziki
- Atiku ya bayyana duk jawabin da tsohon gwamnan na jihar Lagas ya yi game da arzikinsa a matsayin shirme zalla
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya bukaci abokin hamayyarsa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya fito waje ya fadi tushen arzikinsa, Nigerian Tribune ta rahoto.
A hirarsa da BBC a ranar Talata, Tinubu ya ce ya gaji gidaje wanda hakan ya taimaka sosai wajen dukiyar da ya tara.
Tsohon gwamnan na jihar Legas ya kuma alakanta kansa da biloniyan Amurka, Warren Buffet.
Tinubu ya ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Su basu son dukiya ne, idan basu son dukiya-kasuwanci na kawo riba. Na bayar da misali da Warren Buffet, daya daga cikin mutane mafi arziki a Amurka da duniya. Ya fara ne da siyan hannun jari. Na gaji gidaje, na juya kadarorin.
"Ba na karyata dukiyata. Nine gwamnan da aka fi bincike tsawon shekaru takwas har zuwa 2007. Tun da na bar karagar mulki, ina nan kuma har yanzu, ban karbi wani mukami na gwamnati ba, babu kwangilar gwamnati."
Ta yaya wanda ya fito daga gidan talakawa zai gaji dukiya, Atiku ga Tinubu
Sai dai kuma a cikin wata sanarwa daga Phrank Shaibu, mai bashi shawara kan harkokin sadarwa, Atiku ya kalubakanci Tinubu a ranar Lahadi kan ya fito ya bayyana tushen arzikinsa.
Jaridar Daily Trust ta nakalto yana cewa:
"Shakka babu ya kauce lokacin da wakilin BBC ya tambaye shi kan ya bayyana tushen arzikinsa, dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya amsa da tambaya, "Kai makiyin arziki ne? Daga baya ya bayar da labarin kanzon kurege kan yadda ya gaji dukiyarsa da kuma siyan hannun jari kamar Warren Buffet. Wannan shirme ne gaba daya.
"Abun mamaki, Tinubu ya fada ma kwamitin majalisar dokoki na jihar Lagas da aka kafa don binciken karatunsa a 1999 cewa bai iya kammala makarantar sakandare ba saboda gidansu talakawa ne.
"Gwamnan ya magantu game da wahalar da ya sha yana matashi da yadda ya tsallake gwagwarmayar duniya. Bayan kammala karatunsa na firamare, gwamnan ya ce ya samu gurbin karatu a makarantar sakandare amma bai iya ci gaba da karatunsa ba saboda talauci. Sai da ya kama sana'ar hannu kafin ya garzaya kasar Amurka don neman madafa,
"Don haka ta yaya, wanda danginsa suka kasa tura shi makaranta saboda talauci duk da tsarin karatu kyauta a lokacin, ya gaji dukiyoyi daga wannan ahlin? Wannan shirme ne. Tinubu zai yin nisa idan ya daina hada kansa da Warren Buffet wanda hukumomin Amurka ba su taba alakanta tushen arzikinsa da miyagun kwayoyi ba."
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma bayyana cewa ba yanzu aka fara dasa ayar tambaya a kan dukiyar Tinubu ba.
Zan iya muhawara daga safe har dare, Tinubu ya magantu
A wani labarin, Bola Tinubu ya yi martani ga abokan hamayya da ke zarginsa da kaucewa yin muhawara da sauran masu neman takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023.
Tinubu ya ce zai iya tsayawa a fafata da shi daga safe har dare amma dai ba da wadanda ke neman yin kudi da shi ba.
Asali: Legit.ng