Ba Wata barazana Da Atiku Zai Yiwa Tinubu A Yankin Arewa maso Gabas
- Jam'iyyar APC na yawan sukar 'dan takarar jam'iyyar PDP na shugaban 'kasa Alhaji Atiku Abubakar
- Lawan wanda yake a matsayin mai kula da hada-hadar kamfen din Tinubu a jihar gombe yace wasa ne ace Atiku zai kawo jahohin arewa maso gabas
- Atiku Abubakar ya fito ne daga yankin arewa maso gabas, yayin da mataimakin Tinubu ma ya fito daga yankin arewa maso gabas
Gombe: Lawal Bayero shi ne kodinetan matasan jam’iyyar APC a jihar Gombe kuma mamba a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar (PCC) mai wakiltar Arewa maso Gabas.
A wata zantawa da manema labarai a jihar Gombe wanda cikinsu harda jaridar The Nation ya bayyana abubuwa masu yawa game da shirinsu kan zaben, ga yadda tattaunawar tasu ta kasance
Matar Tinubu Tace Nan Gaba Za'ai Takarar Kirsita da Kirsita, Amma Yanzu Lokacin Muslmi Da Musulmi Ne
A matsayinka na ko’odinetan yakin neman zaben Tinubu na jihar Gombe, yaya za ka kwatanta kokarin da kake yi?
"Zan bayyana wannan matsayin a matsayin babban nasara da kuma nuni da cewa muna kan hanya samun nasara a 2023.
"Kuna iya ganin yadda dimbin matasa ke fitowa wajen yakin neman za'bensa".
"Ina da yakinin cewa APC na da tabbacin samun nasara a babban zabe mai zuwa. Ni bana ganin wani dan takara da kara da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, gaskiya babu".
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayero ya cigaba da cewa:
"Muna da mafi yawan gwamnoni da Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai da ‘yan majalisar jiha a fadin kasar nan, kuma duk wadannan sun lashi takobin tabbatar da nasarar Tinubu a zabe mai zuwa".
Nasarar Tinubu na nufin haɗin kai, da kuma tabbtar da Nigeria 'daya, sannan kuma Tinubun nan ya tallafawa 'yan arewa da yawa wajen cika burukansu, yanzu shima lokaci ne da za'a rama masa".
Jam’iyyarmu ta dogara ne da irin karfin da matasa ke da shi a kasar nan".
"Rahotanni sun bayyana cewa al’ummar Najeriya kusan kashi 75 cikin 100 matasa ne kuma muna da kaso mai tsoka na adadinsu a jam’iyyar mu".
"Maganar gaskiya idan babu matasa babu APC, akwai shirye-shirye da muke yiwa Tinubu da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya tanadi a wannan babban zaben". .
Atiku ya fito daga yankinku, ta yaya kuke da tabbacin cewa Tinubu zai samu galaba a Arewa maso Gabas a zabe?
Atiku bazai bawa Tinubu a Arewa maso Gabas ruwa ba
"Me Atiku ya yi wa yankin a shekaru takwas da ya yi yana Mataimakin Shugaban kasa a yankin?
Ku dubi hanyar Gombe zuwa Yola, haka take tun zamanin Atiku a matsayin mataimakin shugaban kasa. Abin kunya ne ga Atiku cewa babbar hanya daya tilo da ta hada jiharsa da sauran sassan kasar nan ba ta da kyau, har yanzu tana nan a lalace".
A baya dai yankin Arewa maso Gabas ya kasance tungar Atiku domin babu wani 'dan Arewa maso Gabas a zaben amma yanzu da fitowar Sanata Kassim Shettima labari ya canja, Kamar yadda Lawan ke Masa tambayar.
"Ina da karfin gwiwa domin ban taba ganin mai son yankin Arewa maso Gabas kamar Bola Ahmed Tinubu ba".
"A shekarar 2007, mun ga yadda ya goyi bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a yanzu, Atiku Abubakar ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Action Congress, ya kuma ba shi goyan baya".
"Abin takaici bai yi nasara ba. A 2011 ma ya yi irin wannan abu da dan uwanmu dan jihar Adamawa da Atiku, Malam Nuhu Ribadu, a matsayin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar ACN a 2011".
"A 2015, mun san cewa ba tare da goyon bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ba. Da shugaba Buhari ba zai kai ga nasara har yai kuma sake maimaitawa a 2019".
Ya goyi bayan Atiku Abubakar daga jihar Adamawa, ya goyi bayan Nuhu Ribadu daga jihar Adamawa sannan ya dauko Kassim Shettima daga jihar Borno.
Ban taba ganin babban masoyin Arewa maso Gabas a kasar nan kamar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ba. Ko a da da yake yin nasara a jihar Gombe, yanzu ta na hannun jam'iyyar APC, to ya zai yi?
Ba wai gwamnan jihar ne kadai ba, har da Daraktan yankin Arewa maso Gabas na kungiyar yakin neman zaben shugaban kasan Tinubu da Sanata Kassim Shettima duk suna gombe.
Lawan ya cigaba da amsa tambayar da cewa:
"Don haka muna da jahohi uku a yankin. Saboda mugun aikin da jam’iyyar PDP ta yi a jihar Taraba kowa yana addu’ar samun sauyi".
"Sai kuma Adamawa da Bauchi da suka shafe shekaru hudu suna hannun PDP. Duk mun san cewa mun rasa Adamawa da Bauchi ne sakamakon rigingimun cikin gida a APC kuma a shirye muke mu gyara gidanmu, mun gana da masu ruwa da tsaki kuma sun sha alwashin hada kai domin samun nasarar Asiwaju".
Me yasa Kake bawa Gwamna Inuwa Yahaya goyon baya a karo na biyu?
"Muna goyon bayansa saboda ya yi dakyau".
Ku zagaya jihar za ku ga yadda ya taba rayuwar al’umma ta hanyar shirye-shiryen bunkasa rayuwa. Dubi rukunin masana'antu na Dadinkowa, kalli fannin ilimi wanda a yanzu ya ba da damar gyara sabgar. Aikin ‘Gombe go green project’ yanzu haka yana dasa itatuwa a fadin jihar da kuma aikin gina tituna kilomita 100 a dukkanin fadin kananan hukumomin jihar goma sha daya".
Ina yi masa godiya a kan haka domin sabuwar hanyar sadarwa ta hada yankunan mu da birni.
Menene ra'ayinku kan halin da matasa suke ciki a Najeriya baki daya?
Idan ka duba a kusa da mu, yawancin masana'antun mu ba sa aiki. Waɗanda muka sani tun cikin 70s, 80s da 90s ba su nan.
Ya kamata shugabanninmu su tashi su yi wani abu a kan lamarin saboda tabarbarewar tsaro. Akwai karin maganar da ake cewa "hannun banza abokin aikin shaidan ne".
Halin da matasan mu ke ciki a halin yanzu ya taimaka kan matsalar tsaro. Wannan ya yi kama da abin da muke ciki game da tashe-tashen hankula a Arewa maso Gabas da ’yan fashi a Arewa maso Yamma.
Lokacin da aka samu tsaro ne manoma za su iya zuwa gonakinsu, su ma matasa za su samu aikin yi.
Idan muna da tsaro, za mu iya gayyatar abokanmu da ke Turai su zo su zuba jari a cikin kasarmu, saboda dimbin filaye a kasar da kuma arha arha.
Don haka a wannan karon, ba na son matasan kasar nan su yi kuskure. Dole ne matasa su tashi tsaye su zabi Tinubu domin shi ne na matasa.
Mu dauki misali da yadda ya taso da Fashola, ministan ayyuka, Rauf Aregbesola, ministan harkokin cikin gida, Muiz Banire, tsohon mai baiwa jam’iyyar mu shawara kan harkokin shari’a, tsohon gwamna Ambode na jihar Legas.
Ga gwamnan jihar na yanzu Sanwolu wanda shi ma matashi ne. Zan iya gaya muku cewa yanzu lokaci ne na "duk wanda yaci ladan kuturu...".
Ba mu da tantama kan iyawar Asiwaju wajen baiwa matasa kyauta. Ba mu da shakku a cikin soyayyar da yake yi wa matasa, ya yi a baya kuma zai sake yi.
Asali: Legit.ng