Yadda Mata da Mijinta Su Ka Kusa Shiga Takarar Kujerar Majalisar Dattawa Tare
- A ‘yan shekarun baya-bayan nan, an samu wasu mata sun fara shiga siyasar Najeriya, ana damawa da su
- Amma dai ba kasafai aka saba ganin mata da miji duk su na siyasa, har ta kai su na neman takara ba
- Emmanuel Uduaghan da matarsa, Natasha Akpoti Uduaghan sun kwallafa rai a kujerar Majalisar dattawa
Emmanuel Uduaghan ya yi niyyar sake neman takarar Sanata a jihar Delta, amma ta tabbata matarsa za tayi takara a Kogi ta tsakiya a 2019.
Natasha Akpoti-Uduaghan
A zaben 2019, Natasha Akpoti-Uduaghan ta nemi Sanata mai wakiltar mazabar jihar Kogi ta tsakiya a karkashin jam’iyyar hamayya ta SDP.
Kamar yadda ta sha kashi a zaben Gwamna a 2015, ‘yar siyasar ba ta iya kai labari a zaben ba.
A watan Mayun 2022, Natasha Akpoti-Uduaghan ta lashe zaben tsaida gwani na ‘dan takarar majalisar dattawa, wannan karo a jam’iyyar PDP.
Matar Tinubu Tace Nan Gaba Za'ai Takarar Kirsita da Kirsita, Amma Yanzu Lokacin Muslmi Da Musulmi Ne
Legit.ng Hausa ta fahimci matar tsohon Gwamnan za ta gwabza da Sanata Abubakar Ohere na jam’iyyar APC da sauran ‘yan takara a zaben 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Akpoti ta doke Mamud Attah da kuri’u 159 da 13 a zaben tsaida gwanin da aka shirya. Ko da aka je kotu, 'yar siyasar mai shekara 43 ce tayi nasara.
Emmanuel Uduaghan
Emmanuel Uduaghan wanda ya yi Gwamna a jihar Deleta tsakanin 2007 da 2015 ya yi takarar majalisar dattawa a karkashin APC a zaben 2019.
Daga baya Emmanuel Uduaghan ya bar jam’iyya mai mulki, ya dawo inda aka san shi watau PDP, domin ya kuma jarraba sa’ar zama Sanata a 2023.
Bayan ya yi ta musanya rade-radin cewa ba zai nemi Sanatan Delta ta Kudu ba, a karshe Uduaghan ya hakura da takara, ya yi murabus daga yin siyasa.
Amma da farko ‘dan siyasar ya yi ta nuna ba zai janye takara ba, da shi za a gwabza a zaben badi.
Natasha Akpoti tana rike da sarautar Ohi’ogu ta kasar Ebira shi kuwa Mai gidanta Cif Emmanuel Oritsejolomi Uduaghan shi ne Aleman mutanen Warri.
Babu ruwan mai dakina da mulki - AKY
A lokacin da ake zargin iyalan Gwamna mai-ci da katsalandan a harkar mulki, an ji labari Abba Gida-Gida yace ba zai bari ayi haka ba idan ya ci zabe.
Muddin Abba Kabiru Yusuf da NNPP suka karbi Gwamnatin jihar Kano, za a soke ofishin uwargidar Gwamna da aka fito da shi bayan zaben 2019.
Asali: Legit.ng