Sumbatar Mata A Fim Ne Kawai Gudunmawar Ka Ga Ibo, Ulasi Ya Ragargaji Kakakin Kamfen Ɗin Peter Obi
- Dan Ulasi, kakakin kamfen din takarar Atiku Abubakar a kudu maso gabas ya ragargaji kakakin kamfen din Peter Obi, Kenneth Okonkwo, kan kiransa dan maula
- Ulasi, ya ce Okonkwo ba shi da wani gudunmawa da ya bawa kabilar ibo illa yin fim da sumbutar mata a cikin fim
- Ulasi ya ce shi kam yana cikin wadanda suka yi wa ibo sadaukarwa ta hanyar yakin Biafra har ya rasa hannu daya
Jagoran kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na PDP a kudu maso gabas, Dan Ulasi, ya ragargaji kakakin kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na Labour Party, Kenneth Okonkwo, rahoton The Nation.
A baya-bayan nan, Okonkwo ya kira Ulasi dan maula, ya zarge shi da cin amanar kabilar Ibo ta hanyar goyon bayan dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma, Ulasi, yayin da ya ke magana a shirin kakkaki na AIT, kafar da Okonkwo ya yi maganar, shima ya soke shi da cin amanar Ibo.
Ya ce lauyoyin PDP suna duba zargin da ya yi wa dan takarar shugaban kasar yana mai cewa:
"Lauyoyin mu na duba lamarin. Ba zai tafi ... Ina son in ga kwarewarsa a matsayin lauya a kotu a lokacin da ya dace."
Ulasi ya ce, akasin Kenneth Okonkwo wanda kawai fim ya ke yi sai sumbatar mata, shi ya yi sadaukarwa ga ibo don ya yi yakin Biafra inda ya rasa hannunsa daya.
Shugaban kamfen din na kudu maso gabas ya ce:
"Na yi wa mutane ne sadaukarwa. Duk ranar da na hadu da Kenneth Okonkwo, zan tambaye shi shekarunsa, gudunmawar da ya bawa ibo?"
"Menene gudunmawarsa bayan yin fim da sumbatar mata a talabijin muna kallo? Na yi wa Biafra yaki. Idan shi bai yi yaki ba, iyayensa sun yi yaki?
"Ina da hannu daya, ba zan iya amfani da wannan hannun ba. Amma ya zo ya kira ni dan maula. Na bogi, yana kira na dan maula?
"Wane gudunmawa ya bawa mutanen mu? Babban abin da mutanen Ibo suka gani a kasar nan shine yakin basasa. Ya bada gudunmawa? Ya yi yaki?".
Okowa da Atiku sun janye daga tattaunawar takarar shugaban kasa
A wani rahoton, dan takarar shugaban kasa na APC, Atiku Abubakar da mataimakinsa, Ifeanyi Okowa na jihar Delta sun janye daga taron tattaunawa da yan takarar shugaban kasa da Daria Media ta shirya.
Sanarwar da aka fitar ta ce sun janye ne saboda wasu dalilai da ba a fayyace su ba a cikin sanarwar.
Asali: Legit.ng