Atiku Da Okowa Sun Janye Daga Taron Tattaunawa Da Yan Takarar Shugaban Kasa

Atiku Da Okowa Sun Janye Daga Taron Tattaunawa Da Yan Takarar Shugaban Kasa

  • Democratic Party, PDP, Atiku Abubakar da abokin takarsa Ifeanyi Okowa sun janye taron tattaunawa da yan takarar shugaban kasa a 2023
  • Kafar watsa labaria ta Daria Media da hadin gwiwar News Central da gidan talabijin na kasa NTA da wasu ne suka shirya taron tattaunawar mai lakacin 'The Candidates'
  • Manufar wannan taron shine bawa yan takarar shugabannin kasar dama su taho su amsa tambayoyi da yan kasa ke da shi tare da tallatawa mutane tsare-tsaren da suke shirin yi idan an zabe su

Abubakar Atiku, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, da abokin takararsa, Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta, a ranar Talata sun janye daga taron jin ra'ayoyin al'umma da aka shiryawa masu neman takarar shugaban kasa a 2023.

An sanar da hakan ne cikin wani rubutu a shafin Tuwita da Gidan Talabijin na Kasa, NTA, ta fitar.

Kara karanta wannan

2023: PDP Ta Yi Watsi da Gwamnonin G-5, Zata Ci Gaba Da Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa a Wata Jihar Arewa

Atiku da Okowa
Atiku Da Okowa Sun Janye Daga Taron Tattaunawa Da Yan Takarar Shugaban Kasa. Hoto: @daily_trust.
Asali: Facebook

Daria Media tare da hadin gwiwar News Central, da Gidan Talabijin na kasa, NTA, da wasu ne suka shirya tattaunawar da yan takarar shugaban kasa mai lakabin 'The Candidates'

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

NTA din ta ce:

"Saboda wasu dalilai, Alhaji Atiku Abubakar da abokin takararsa, Dr Ifeanyi Okowa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ba za su samu zuwa taron tattaunawa da yan takarar shugaban kasa ba."

Wannan ba shine karo na farko da Atiku zai gaza halartar taron da aka shiryawa yan takarar shugaban kasa ba.

A farkon wannan watan, ya bukaci abokin takararsa ya wakilce shi a wani taron tattaunawa da Cibiyar Cigaban Demokradiyya, CDD, tare da hadin gwiwar Arise Television suka shirya.

A watan Oktoba, Atiku kuma bai halarci wani taro ba da Women Radio 91.7 ta shirya wa manyan yan takarar shugaban kasa a dakin taro na NAF Centre da ke Abuja.

Kara karanta wannan

2023: Ku Yi Hattara Da Peter Obi, Kungiyar Matasan Kirista Ta Aike Da Sako Mai Karfi Ga Yan Najeriya

Tinubu, Atiku Sun Gagara Halartar Taron ‘Yan Takara, Kwankwaso, Obi Sun Yi Kasuwa

A baya, kun ji cewa biyu daga cikin manyan masu neman mukamin shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu da Atiku Abubakar ba su halarci taron ‘yan takara ba.

Premium Times ta kawo rahoto a daren Litinin, 6 ga watan Nuwamba 2022 cewa Gwamna Ifeanyi Okowa ya samu wakiltar Atiku Abubakar na PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel