Tinubu Na Tiƙa Rawar 'Buga' A Gidan Giya A Landan Yayin Da Ƴan Arewa Suna Can Suna Mutuwa, In Ji Farfesa Usman

Tinubu Na Tiƙa Rawar 'Buga' A Gidan Giya A Landan Yayin Da Ƴan Arewa Suna Can Suna Mutuwa, In Ji Farfesa Usman

  • Tsohon shugaban hukumar NHIS, Farfesa Usman Yusuf ya yi tir da rawar da Tinubu da tawagarsa suka tafi Landan suna yi
  • Farfesa Yusuf, ya bayyana hakan a matsayin rashin damuwa da halin da yan kasa ke ciki musamman yan arewa da ke fama da matsalar tsaro
  • Yusuf ya ce za su dauki wannan bidiyon na Tinubu da tawagarsa 'suna sharholiya a Landan' su nuna wa mutanen arewa don su san irin mutanen da ke neman shugabancin su

Arise TV - Farfesa Usman Yusuf, tsohon hukumar inshoran lafiya na kasa, NHIS, ya zargi Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC, da rashin damuwa da halin da yan Najeriya ke ciki, musamman yan arewa.

Bola Tinubu
Tinubu Na Tiƙa Rawar 'Buga' A Gidan Giya A Landan Yayin Da Ƴan Arewa Suke Mutuwa, In Ji Farfesa Usman. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Ya bayyana hakan ne a matsayin martani kan bidiyon da wasu yan tawagar Tinubu a Landan suka wallafa a soshiyal midiya.

Kara karanta wannan

2023: Na Shirya Muhawara Daga Safe Har Dare, Tinubu Ya Maida Zazzafan Martani

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A bidiyon, an ga Tinubu a yanayi na murna bayan jawabinsa da ya yi a Chatham House a Landan.

An ga Tinubu, zagaye da tawagarsa yana rawa a yayin da ake saka fitaciyyar wakar 'Buga' ta Kizz Daniel.

An ga Dave Umahi, gwamnan Jihar Ebonyi; Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, Dr Kayode Fayemi, tsohon gwamnan jihar Ekiti suna rawa a cikin bidiyon.

Martanin Farfesa Yusuf

Farfesa Yusuf, yayin hirar da aka yi da shi a Arise TV, ya soki abin da suka yi.

Ya ce:

"Mu a arewa daga Adamawa zuwa Zamfara, muna birne gawarwakin mutane da aka kashe mana. Shi kuma mutumin da ke fatan zama shugaba da tawagarsa, suna gidan giya a Landan, suna rawar Buga kuma muna daukan wannan bidiyon muna nuna wa mutanen mu... Muna shan wahala.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Harbe Fitaccen Malami, Sun Yi Garkuwa da Tsohuwar Akanta Janar da Wasu Mutane Uku

"Yanzu na dawo daga Katsina, na yi magana da yan sansanin gudun hijira, na ga wahalan da mutanen mu ke sha. Wadannan sune shugabannin ku."

Bidiyon Tinubu Yana Rawar Buga Bayan Taron Landan

Tunda farko, kun ji cewa wani sabon bidiyon Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ya fito, inda ya ke kwasar ruwar 'Buga' yana nishadi tare da tawagarsa.

Tinubu tare da yan tawagarsa da suka kunshi gwamnoni da manyan yan siyasa da suka masa rakiya zuwa Landan sun taka rawa yayin da wasu ke cin abinci.

Bisa dukkan alamu Tinubu da yan tawagarsa suna cikin farin ciki da nishadi bayan taron da aka yi a Chatham House.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164