'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Tsohon Akanta Janar Da Wasu Mutane Uku

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Tsohon Akanta Janar Da Wasu Mutane Uku

  • Yan bindiga sun yi awon gaba da tsohuwar Akanta Janar ta jihar Kuros Riba tare da wasu mutane uku da yammacin Talata
  • Lamarin ya faru Awanni 24 da aka ji rundunar 'yan sandan jihar na cewa ta girke dakaru a kan babban Titin don kare al'umma
  • Bayanai sun nuna cewa maharan sun harbi wani fitaccen Malami a harin wanda yanzu haka yana kwance a Asibiti

Cross River - Tsohuwar Akanta Janar a jihar Kuros Riba lokacin mulkin Donald Duke, Misis Rose Bassey, da wasu mutane uku da ba'a gano bayanansu ba sun shiga hannun masu garkuwa da mutane.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an yi garkuwa da su ne da yammacin ranar Talata a yankin Uyanga-Ikomita dake babban Titin Kalaba zuwa Ikom.

Yan bindiga.
'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Tsohon Akanta Janar Da Wasu Mutane Uku Hoto: vanguard
Asali: Twitter

Wasu 'yan bindiga ne suka yi garkuwa da su a kan babban Titin mai yawan tara matafiya bayan sun bude wa motoci wuta domin tilasta masu tsayawa

Kara karanta wannan

Da Duminsa: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Wuse Zone 5, Sun Sheke Mutum 1, An Nemi Wasu An Rasa

An tattaro cewa yayin harin yan bindigan sun harbi wani shahararren Malami, Evangelist Edim Edim Omin, amma bisa sa'a ya yi nasarar tsira daga sharrinsu, yanzu haka yana kwance a Asibiti.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bincike ya nuna tsohouwar Akanta Janar ɗin na tare da Direbanta kuma dukansu aka haɗa aka yi gaba da su da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin Talata, kamar yadda Sunnews ta ruwaito.

Bayanai sun nuna cewa lamarin ya rutsa da su ne yayin da suke kan hanyar dawowa daga gonar Misis Rose Bassey dake Ekpri Iko bayan Iwuru a ƙaramar hukumar Biase.

Wane mataki hukumomin tsaro suka ɗauka?

Wannan na zuwa ne awanni 24 bayan hukumar 'yan sandan jihar tace ta tura tawagar dakaru ta suka hada masu yaki da kungiyoyin asiri da garkuwa da mutane domin baiwa matafiya tsaro a babban Titin.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kassara 'yan ta'adda, sun ragargajiya maboyar 'yan bindigaa dazukan wata jiha

Yayin da wakilin jaridar ya ziyarci wurin da safiyar Laraban nan da muke ciki ya ga Jami'an yan sanda tawaga-tawaga a wurare daban-daban a kan babban Titin.

Haka zalika da aka tutubi jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda, SP Irene Ugbo, ya tabbatar da faruwar lamarin. Yace suna kan kokarin ceto mutanen huɗu.

Kwamishinan Da Yan Bindiga Suka Sace Ya Shaki Iskar Yanci

A wani labarin kuma Kwamishinan gidaje da raya birane na jihar Benuwai wanda aka yi garkuwa da shi ya kubuta

Mashawarci na musamman ga gwamna Samuel Ortom kan harkokin tsaro ne ya tabbatar da kubutar kwamishinan ranar Talata.

Sai dai yace nan ba da jimawa ba gwamnatin jihar zata fitar da sanarwa mai ɗauke da cikakken bayani kan yadda Allah ya tseratar da jigon.

Asali: Legit.ng

Online view pixel