Kanawa Sun Gaji da Mulkin Molon Ka Na Jam’iyyar APC, Inji Dan Takarar Gwamnan NNPP

Kanawa Sun Gaji da Mulkin Molon Ka Na Jam’iyyar APC, Inji Dan Takarar Gwamnan NNPP

  • Dan takarar gwamna a jihar Kano ya caccaki gwamna Ganduje, ya ce Kanawa sun gaji da mulki mara dadi na APC
  • Abba Yusuf ya bayyana manufofin da yake son cimmawa idan ‘yan Kano suka zabe shi a 2023; zaben badi
  • Ya kuma kaddamar da abokin takararsa, inda ya bayyana aniyarsa ta sake ciyar da jihar Kano gaba

Jihar Kano - Dan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar NNPP, Alhaji Abba Yusuf ya ce jama’ar jihar Kano sun gaji da mulkin jam’iyyar APC mai ci a yanzu.

Hakazalika, ya bukaci gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar da ya mika wa NNPP mulkin jihar a 2023 domin tafiyar da ita cikin sauki kuma yadda ya dace.

Ya kuma bayyana cewa, idan ya gaji Ganduje a zaben mai zuwa, zai ci gaba da ayyuka ne kamar yadda tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi a baya.

Kara karanta wannan

An Ga Minista Mai Karfi a Mulkin Buhari a Bidiyo Yana Tinkahon Yadda Za Su Ci Zabe

Abba Yusuf ya caccaki Ganduje
Kanawa Sun Gaji da Mulkin Molon Ka Na Jam’iyyar APC, Inji Dan Takarar Gwamnan NNPP | Hoto: headtopics.com
Asali: UGC

Abba Yusuf ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Kano a gaban ilahirin mambobi da magoya bayan jam’iyyar NNPP, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abba Yusuf ya bayyana manufofinsa, ya kaddamar da abokin takararsa

Ya bayyana ne a gabansu domin kaddamar da manufofin da yake son ya cimma da kuma ayyukan da zai yiwa Kanawa idan aka zabe shi.

Ya kuma yi amfani da wannan daman wajen bayyana abokin takararsa, Aminu Abdulsalam.

Da yake jawabi, ya bayyana cewa, zai yi aiki wajen inganta tattalin arziki da harkar kasuwanci a jihar Kano tare da sanya ta amsa sunanta cibiyar kasuwanci.

Ya kuma bayyana cewa, zai yi aiki tukuru wajen farfado da kamfanoni da masana’antu a jihar.

Daga nan ya bayyana yadda ya fito a matsayin dan takarar gwamnan jam’iyyar NNPP bisa turbar dimokradiyya.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ya Kara Shiga Tasku, Wani Jigo Da Ya Nemi Takarar Gwamna a APC Ya Koma PDP

A watan Yunin bana ne Kabir Abba Yusuf ya fito a matsayin dan takarar gwamnan NNPP bayan gudanar zaben fidda gwani a jam'iyyar, rahoton This Day.

NNPP ta karyata jita-jitan ta kulla kawance da jam'iyyar PDP gabanin zaben 2023

NNPP ta ce ba za ta daga kafa kan kowane dan takarar shugaban kasa, kuma za ta ci gaba da gangami don tabbatar Kwankwaso ya zama shugaban kasa.

An yada jita-jitan cewa, jam'iyyar NNPP ta hada gwiwa da jam'iyyar PDP gabanin zaben 2023 mai zuwa.

Jam'iyyun siyasa na ci gaba da caccakar juna da kuma musayar yawu gabanin babban zaben 2023 mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.