Jonathan Ya Bude Baki Ya Yi Magana Kan Takara a APC da Sake Neman Mulki

Jonathan Ya Bude Baki Ya Yi Magana Kan Takara a APC da Sake Neman Mulki

  • Nathaniel Bivan ya rubuta littafin game da rayuwar Obioma Onwuzurumba a cocin fadar Aso Villa
  • A hirar da aka yi da Dr. Goodluck Jonathan a littafin, ya nuna ya gama tsayawa takara a Najeriya
  • Jonathan yace batawa kansa suna ne ya dawo siyasa, ya rika yawo yana rokon mutane su zabe shi

FCT, Abuja - Har abada tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ba zai sake tsayawa neman takarar kujerar shugaban kasa a Najeriya ba.

Jaridar Punch a wani rahoto na ranar Alhamis, tace Goodluck Jonathan ya nesanta kansa daga neman takara bayan ya yi shekaru biyar a mulki.

Dr. Jonathan yana ganin wani yunkurin zama shugaban Najeriya zai zubar masa da kima.

Tsohon shugaban ya yi wannan bayani a hira da aka yi da shi, hirar na cikin littafin tarihin Obioma Onwuzurumba da Nathaniel Bivan ya rubuta.

Kara karanta wannan

Fata-fata Kenan: Jama'a Sun Dauki Dumi Bayan Ganin Wani Kalan Takalmi Da Peter Obi Ya Sanya A Wurin Taro

Obioma Onwuzurumba ya kaddamar da littafin da ya kunshi labarin zamansa a matsayin Limami a cocin fadar shugaban kasa a garin Abuja.

Jonathan wanda ya rike shugabancin Najeriya bayan rasuwar Ummaru ‘Yar’adua tsakanin 2010 da 2015 yace shi da Aso Villa sai dai kaddara.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jonathan
Goodluck Jonathan da Shugaban kasa mai-ci Hoto: Bashir Ahmaad
Asali: Twitter

Sai dai kaddarar Ubangiji - Jonathan

“Idan aka wayi gari aka ga na sake zama shugaban kasar Najeriya, hakan yana nufin wani abin ne da ya fi karfi na ya faru.
Amma ba zan je sayen fam, ina lallabar jama’a da yawon kamfe ba; Ba zan sake wannan ba, idan nayi, na zubar da kima ta.”

- Dr. Goodluck Jonathan

Jonathan zai yi takara a APC?

An rahoto Jonathan din yana cewa ya ji dadin yadda aka yi ta rade-radin ya saye fam din neman zama ‘dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Kasa Ya Fadi Babban Abin da Yake Sa Jami'ai Tafka Sata a Gwamnati

“Na ji dadin hayaniyar da aka rika yi. Akalla ba ci mani mutunci suka yi ba. Tun da dai fatattaka ta aka yi daga kan mulki, aka ce na gaza.

Yanzu kuma ‘Yan Najeriya suna cewa, ‘Oh, wannan mutumi ya dawo’, hakan yana nufin an wanke ni. Saboda haka na ji dadin hayaniyar.”

Jonathan yace an yi ta damunsa da tambaya, har da Jakadun kasashen Duniya, amma yace bai tunanin zai shiga wata takarar a PDP ko APC.

Tsakanin Tinubu, Atiku, Obi da Kwankwaso

Rahoto ya zo cewa Jakadar kasar Birtaniya ta hadu da Shugaban Jam’iyyar APC a Sakatariyarsu a Abuja, ta ja kunne kan murde zaben da za ayi a 2023.

A wajen Catriona Laing da kasar Ingila, babu bambanci tsakanin Bola Tinubu, Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso na APC, PDP, LP da NNPP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng