Na Shirya A Yi Kare Jini Biri Jini Dani A Zaben 2023 Mai Zuwa, Inji Tinubu

Na Shirya A Yi Kare Jini Biri Jini Dani A Zaben 2023 Mai Zuwa, Inji Tinubu

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya nuna shirinsa na shanye duk kazantar da ke tattare da siyasa
  • Ya bayyana cewa tun bayan mika mulki ga farin hula a Najeriya yake kira ga zabe na gaskiya da amana
  • Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya ce ya shirya kuma daidai yake da duk wanda yayi kokarin yin kazamar arangama da shi

Landan - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressive Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa ya shirya yin siyasar kare jini biri jini.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 5 ga watan Disamba, yayin da yake zantawa da yan Najeriya mazauna waje a Chatham House da ke Landan, kasar Birtaniya, jaridar Punch ta rahoto.

Bola Tinubu
Na Shirya A Yi Kare Jini Biri Jini Dani A Zaben 2023 Mai Zuwa, Inji Tinubu Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Da yake amsa tambayoyi daga bangaren jama'a, tsohon gwamnan na jihar Lagas ya bayyana cewa duk kokarin da abokan hamayya ke yi na dasa ayar tambaya kan makarantarsa bai cimma nasara ba.

Kara karanta wannan

Jigon APC Da Ke Goyon Bayan Peter Obi Ya Bayyana Inda Za Su Koma Idan LP Ta Sha Kaye A 2023

Wani bangare na jawabin nasa na cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Kwarai da gaske, idan kana son dambe da alade, dole ka shirya zama da kazanta. Wannan shine abun da nake yi. Na shiga siyasa tare da sanin cewa cike yake da ruwan kwatami. Hayaki zai taso kuma dole ka zauna da dattin sannan ka tabbatar da ganin cewa ka tsaya tsayin daka don gama aikin."

A bar yan Najeriya su zabi wanda suke so ya kula da harkokin kasarsu a 2023

A jawabinsa na bude taro, Tinubu ya nuna matsayinsa a kan rikicin zabe da tsoratarwa yayin da ya bukaci sauran masu takarar shugaban kasar da su bari yan Najeriya su yanke hukunci a kan makomar kasar.

Sunrise ta nakalto yana cewa:

"Na tsaya kyam wajen adawa da duk wani nau'i na rikicin zabe da barazana.

Kara karanta wannan

Bidiyon Tinubu, El-Rufai da Manyan ‘Yan Siyasa Sun Girgijewa Bayan Taron Gidan Chatham a Landan

"Kasancewar na shafe yawancin rayuwata a siyasar adawa, na dade ina yaki akan magudin zabe da duk wani yunkuri na dakile zabin masu zabe. Zan ci gaba da aikata haka, na yi alkawari.
"Ina umurtan daukacin abokan fafatawa na a zaben nan da suma su aikata hakan. A bar muradin mutane ya yanke hukunci kan makomar kasarmu. Kuma a bar masu zabe su yi ra'ayinsu a wannan zaben cikin yanci maimakon bari wasu fitinannu su razanar da al'umma."

Har wayau, Tinubu ya nuna karfin gwiwar cewa nan da yan watanni kadan, mutane za su je wuraren zabe sannan su bashi kuri'unsa.

2023: Baba-Ahmed ya ce Buhari bai damu da takarar Tinubu ba

A wani labarin, Yusuf Datti Baba-Ahmed ya yi ikirarin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bai damu da takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na APC ba ko kadan.

Dan takarar mataimakin shugaban kasar na Labour Party ya ce jam'iyyarsa kadai ce ta yi saura a Najeriya domin a cewarsa farin jinin APC da PDP ya gushe a kasar.

Kara karanta wannan

Shinkenan ta takewa Tinubu, 'yan jiharsa su bayyana dan takarar da za su zaba ba shi ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel