Obi: Na Rasa Me APC Ke Jira Da Bata Sallame Ni Ba – Babachir Lawal

Obi: Na Rasa Me APC Ke Jira Da Bata Sallame Ni Ba – Babachir Lawal

  • Tsohon sakataren gwamnatin tarayya ya bayyana cewa bai san dalilin da yasa APC bata sallame shi ba duk da yana goyon bayan shugabancin Peter Obi
  • Lawal wanda ke goyon bayan dan takarar Labour Party, ya ce idan Obi ya fadi zabe a 2023, za su tattara su koma kasar Kamaru
  • Jigon na APC ya bugi kirji cewa dole Obi ya ci zabe kuma cewa nasararsa abu ne da babu yadda aka iya

Abuja - Tsohon sakataren gwamnatin tarayya kuma jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Injiniya Babachir Lawal, ya jaddada matsayinsa na goyon bayan Peter Obi na Labour Party a zaben shugaban kasa na 2023.

Sai dai kuma, Babachir ya nuna tsananin mamaki cewa jam'iyyarsa ta APC bata sallame shi ba har yanzu duk da ya nuna baya yin dan takararta, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Na Shirye Kazancewa a Siyasar 2023, Dan Takarar Shugaban Kasa Na Sahun Gaba Ya Fusata

Babachir Lawal da Peter Obi
Obi: Na Rasa Me APC Ke Jira Da Bata Sallame Ni Ba – Babachir Lawal Hoto: Babachir David Lawal, Peter Obi
Asali: Facebook

Babachir ya kara da cewar ya zama dole Peter Obi ya lashe zaben shugaban kasa na 2023, duba ga halin da kasar ke ciki a yanzu, jaridar Vanguard ta rahoto.

Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 5 ga watan Disamba, a yayin wata tattaunawa tsakanin Obi da masu ruwa da tsaki na arewa maso gabas a Abuja.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Za mu tattara mu koma Kamaru ida jam'iyyar LP ta sha kaye - Lawal

Babachir ya kuma ce idan jam'iyyar LP ta sha kaye a zaben 2023, Obi da sauran yan jam'iyyar ciki harda shi kansa za su tattara kayansu su koma kasar Kamaru da zama.

Wani bangare na jawabinsa na cewa:

"Ina APC kuma mamba a kwamitin amintattu na jam'iyyar, amma tafiyar Peter Obi/Yusuf Datti nake yi.
"APC bata sallame ni ba tukuna. Ban san me suke jira ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Abokin Takarar Peter Obi Ya Yi Garumin Zargi A Kan Tinubu

"Muna son Obi ya lashe zaben nan kuma dole ya lashe wannan zabe. Idan muka fadi wannan zabe, duk za mu tattara mu koma Kamaru saboda kunya da shan kaye. Ba wai batun ko muna da zabi bane, dole Peter Obi ya lashe zaben nan."

Peter Obi ne wanda yan Najeriya ke bukata

A cewar Babachir, Obi ya cancanta don baiwa yan Najeriya chanjin da suke ta nema tun 2015, rahoton The Eagle Online.

"Cikin sa'a, Peter Obi da abokin takararsa sun cancanta. Muna bukatar jagora don cimma wannan canjin kuma wadannan biyun sun samar da shi.
"Bana yin LP a matsayin jam'iyya. Ina yin Beter Obi ne a matsayin dan takarar shugaban kasa. Ban damu da wacce jam'iyya Peter Obi yake ba, Na ga cewa lokaci ya yi da yan Najeriya zasu samu chanji.
"Sun dade suna ihun neman chanji; ra'ayina shihe cewa Najeriya za ta zabi kowa idan dai ba dan PDP ko APC bane."

Kara karanta wannan

Jami'iyar APC Nakasu Kawai Ta Kawo A Nigeria Tsawon Lokacin da ta Shafe Tana Mulki, Atiku

Dogara ya zama mamba a kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar

A wani labarin, mun ji cewa kwamitin yakin nema zaben shugaban kasa na jam'iyyar PDP, ya nada Yakubu Dogara a matsayin mamba domin fafutukar ganin nasarar Atiku Abubakar a zaben 2023.

Dogara dai ya raba gari da APC da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu kan tikitin Musulmi da Musulmi da dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar mai mulki ya zabi yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng