Ban Taba Sa Rai Ba: Fasto Idahosa Ya Bada Labarin Yadda Kwankwaso Ya Ba Shi Takara

Ban Taba Sa Rai Ba: Fasto Idahosa Ya Bada Labarin Yadda Kwankwaso Ya Ba Shi Takara

  • Isaac Idahosa yace bai taba tunanin zai samu takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar NNPP ba
  • Malamin addinin da ya shiga siyasa yace rana daya, Rabiu Kwankwaso ya kira shi zuwa gidansa a Abuja
  • Idahosa yace a daf da lokacin bada sunayen ‘yan takara zai kure ne ya gana da shugabannin NNPP

Abuja - ‘Dan takaran mataimakin shugaban jam’iyyar NNPP, Isaac Idahosa ya bada labarin yadda ya samu tikiti tare da Rabiu Musa Kwankwaso.

A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin Channels, Bishof Isaac Idahosa yace bai da burin neman kujerar siyasa a lokacin da aka tsaida shi.

Faston yake cewa wata rana ne Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya kira shi a wayar salula, ya nemi ya zo garin Kano domin suyi shagulgulan idi tare.

Kara karanta wannan

Abin da Ya Sa Ba Zan Yarda a Kwantar da ni a Asibitin Gida ba – Atiku Abubakar

Bikin sallar idi a Kano

“Idan kuna so in fada maku yadda abin ya faru, a lokacin hutun sallah, shi (Kwankwaso) ya kira, ni, ‘Bishof, kana ina?’ Na ce ina Legas. ‘Ko za ka iya zuwa Kano muyi bikin sallah tare?’
“Na isa Kano, na iske mutane da yawa. Ya saba ciyar da mutane da-dama da sallah. Sai ya fada mani cewa in gaida mutane, ka san na iya Hausa da kyau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ko ina ya kidime da ihu, bai taba fada mani abin da yake ransa ba. Kusan karfe 12:00 na daren Lahadi sai ya kira ni, saura mako daya INEC ta rufe shafinta.

- Bishof Isaac Idahosa

Bishof Idahosa
Bishof Idahosa da Rabiu Kwankwaso Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Lokaci zai kurewa NNPP

Faston ya shaidawa gidan labaran cewa a ranar Litinin ne NNPP ta gama laluben abokin takara, Idahosa yake cewa lokaci ya kurewa jam’iyyar adawar.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ga Atiku: Ka Zabtare Kudin Makaranta a Jami’arka ko ‘Yan Najeriya da Halarta

"A ranar Laraba, Kwankwaso yace in zo gidansa a Maitama (Abuja) saboda in shiga wajen tantance ‘yan takara, a haka na kama hanya, ban san ni za a tantace ba.
Ina isa sai ga Buba Galadima, shugaban jam’iyya da sauransu. Su kace in zauna, suka tambaye ni burin da nake da shi idan na zama abokin takarar Kwankwaso.
Sai na ce ‘abin da ya kawo ni kenan? Babu wanda ya fada mani na zo nan ne domin a tantance ni. Na dauka ina cikin 'yan kwamitin da za suyi tantacewar ne.

- Bishof Isaac Idahosa

Magana ta tabbata

A nan ne Idahosa ya shaidawa jagororin jam’iyyar cewa bai da wata manufa, illa iyaka zai taimakawa Sanata Kwankwaso wajen samun nasara tare.

Bayan haka sai aka nemi Idahosa ya kawo takardunsa, zuwa daren Laraba sai sunansa ya fara yawo ko ina a kafofin sada zumunta, har lokacin ba ta tabbata.

Kara karanta wannan

"Tarihi Zai Maimaita Kansa" An Faɗi Dan Takaran Da Zai Iya Kasa-Ƙasa da Kwankwaso a Kano a 2023

Daga Alhamis kuwa, ‘dan takaran mataimakin shugaban kasar yace aka yi ta kiran wayarsa, a lokacin Kwankwaso ya fada masa shi ne abokin takararsa.

Tinubu ya ki zuwa wajen taron 'yan takara

An ji labari Atiku Abubakar yana da ra’ayin cewa tsoron amsa tambayoyi a kan zargin badakala ya sa Bola Tinubu ya bar Najeriya, ya tafi kasar Birtaniya.

A wani jawabi daga bakin Kola Ologbondiyan, Atiku yace ‘dan takaran APC a zaben 2023, ba zai iya wanke kan shi daga zargin karyar shekaru da takardu ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng