Atiku Abubakar: Abin da ya sa Bola Tinubu Ya Ruga Ingila, Ya Ji Tsoron Haduwarmu

Atiku Abubakar: Abin da ya sa Bola Tinubu Ya Ruga Ingila, Ya Ji Tsoron Haduwarmu

  • Bola Ahmed Tinubu ya sake kauracewa zaman da aka yi da masu neman takarar shugabancin Najeriya
  • Kwamitin yakin zaben Atiku Abubakar yace ba komai ya jawo hakan ba sai saboda Tinubu na tsoron ‘yan jarida
  • Kola Ologbondiyan yana ganin ‘dan takaran na APC bai da amsoshin tambayoyin da mutane ke shirin yi masa

Abuja - Jam’iyyar PDP tayi magana a kan kauracewa ‘yan jarida da Bola Ahmed Tinubu mai neman shugabancin Najeriya a 2023 yake yawan yi.

Kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, yace Bola Ahmed Tinubu bai son zuwa gaban ‘yan jarida ne a dalilin yunkurinsa na canza birnin tarayya.

The Cable ta rahoto Kola Ologbondiyan yana cewa Bola Tinubu ya tsere zuwa Ingila ne saboda ya gujewa tambayoyi a kan batun canza birnin tarayya.

Kola Ologbondiyan ya yi martani ga Bayo Onanuga wanda ya fitar da jawabi yana cewa ‘dan takaransu ba zai halarci zaman da Arise TV ta shirya ba.

Kara karanta wannan

‘Yan Tinubu Sun Ambaci Jihar Arewa 1 da Za Tayi Wa Atiku Nisa, APC Za Tayi Galaba

Ologbondiyan yace an labe ne da tafiya Ingila

Onanuga ya bada uzuri da cewa Tinubu zai je Birtaniya, inda zai yi wa Duniya bayanin manufofinsa a kan tattalin arziki, tsaro da alakar kasa da kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jawabin martanin Kola Ologbondiyan, yace da gan-gan ‘dan takaran na APC ya bar Najeriya saboda akwai tambayoyin da ake jiran ya bada amsarsu.

Tinubu
'Dan takaran APC, Bola Tinubu Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasar na PDP ya kalubalanci Tinubu da ya zauna da ‘Yan Najeriya, suyi masa tambayoyi a kan manufofinsa.

Ologbondiyan ya dage a kan cewa gwamnatin Tinubu za ta dauke birnin tarayya daga garin Abuja zuwa jihar Legas, yankin da ‘dan takaran ya fito kenan.

Independent ta rahoto kwamitin neman takaran PDP yana cewa bai dace Tinubu ya karyata zancen ba, yana zargin abokan gaba da yi masa sharri.

Kara karanta wannan

2023: APC Ta Nesanta Tinubu da Wani Hoto da Ake Yaɗawa Tare da Shugaban Amurka, Ta Faɗi Gaskiya

Ba iyakar ta kenan ba

An kuma ji kwamitin yana cewa ‘dan takaran na APC yana tsoron ya je wajen ‘yan jarida saboda katobarar da ya saba yi a wajen neman mulkin Najeriya.

“Ta tabbata cewa tafiya zuwa kasar wajen da Asiwaju Tinubu ya kirkiro, saboda ya gujewa tambayoyin da za ayi masa ne a kan shirin canza birnin tarayya...
...da kuma zargin rashin gaskiya da na badakaloli da kuma ta-cewa da aka samu a game da suna, shekaru, nasaba da takardun shaidar karatunsa.

- Kola Ologbondiyan

Zaben 2023 dabam ne

Duk da bai kama sunan wani ‘dan takara ba, rahoto ya zo cewa an fahimci wanda Olusegun Obasanjo yake goyon baya a zaben shugaban kasa na 2023.

Obasanjo ya yi kira da babbar murya ga mutane cewa suyi ta-ka-tsan-tsan da makomar kasa wajen zaben sabon shugaba, yace sai an yi hattara da son zuciya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng