Jerin Jihohi 6 Da Aka Taba Samun Kakakin Majalisa Mace Tun 1999, Arewa Na Da 1

Jerin Jihohi 6 Da Aka Taba Samun Kakakin Majalisa Mace Tun 1999, Arewa Na Da 1

  • Ana yawan korafe-korafe cewa mazan Najeriya na yiwa takwarorinsu mata kafa wajen darewa tare da yin kane-kane a mukaman siyasa a kasar
  • Duk da wannan zazzafan yanayi na siyasar kasar, wasu mata sun samu darewa manyan mukamai kuma hakan na kara haskaka makomar siyasar jinsin a gaba
  • Kimanin jihohi 6 ne suka taba samun mace a matsayin kakakin majalisa tun bayan da Najeriya ta samu yancinta a 1999, a cikinsu daya ce ta fito daga yankin arewa

Tun bayan da Najeriya ta samu yancin kai a 1999, kasar ta samar da kakakin majalisun jiha akalla guda takwas.

A fadin jihohin Najeriya 36, kimanin guda shida ne kawai suka samar da kakakin majalisa mata a majalisun jihohinsu.

Kakakin majalisu mata
Jerin Jihohi 6 Da Aka Taba Samun Kakakin Majalisa Mace Tun 1999, Arewa Na Da 1 Hoto: Olubunmi Adelugba
Asali: Twitter

Ekiti

Jihar Ekiti ita ce ta baya-bayan nan da ta shiga rukunin a kudancin Najeriya. A kwanan nan ne aka zabi Olubunmi Adelugba a matsayin kakakin majalisar jihar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Adelugba ita ce mace ta farko da hau kujerar kakakin majalisa a jihar.

Ta hau kujarer ne bayan tsige Gboyega Aribisogan da mambobin majalisa 17 cikin 25 suka yi a makon da ya gabata.

Ogun

Jihar Ogun wacce ke kudu maso yamma ta samar da Titi Oseni-Gomez a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar tsakanin 2003 da 2008.

Oseni-Gomez ita ce mace daya tilo da ta taba taka wannan matsayi a tarihin jihar.

Anambra

Jihar ce ta samar da kakakin majalisa mata mafi yawa a tarihin Najeriya.

A 2003, Hon. Eucharia Azodo ita ce mace ta farko da ta fara rike mukamin kakakin majalisa a tarihin jihar.=

Jahar ta sake kafa tarihi lokacin da ta samar da Chinwe Nwaebili a matsayin kakakin majalisarta a2011 sannan ta kuma samar da Rita Mmaduagwu a matsayin kakakin majalisa a 2015. An zabi Mmaduagwu ba tare da abokin hamayya ba.

Benue

Benue ce jihar arewa daya tilo da ta taba yin kakakin majalisa mace a tarihin siyasar Najeriya.

Tsakanin 1999 da 2003, mukamin kakakin majalisar jihar na a karkashin ikon Margeret Icheen, wacce ita ce kuma kakakin majalisa mace ta farko a tarihin siyasar Najeriya.

Oyo

Jihar Oyo wacce ita ce hedkwatar siyasar mutanen kudu maso yamma ita ma ta samar da Monsuratu Jumoke Sumonu a matsayin kakakin majalisa mace ta farko a watan Yunin 2011.

Ta yi takara a karkashin rusasshiyar jam'iyyar Action Congress of Nigeria (ACN) kuma ta wakilcin mutanen mazabar Oyo West/East.

Ondo

A watan Mayun 2014 Jumoke Akindele ta zama kakakin majalisar dokoki mace ta farko a jihar Oyo bayan mutuwar magabacinta, Samuel Adesina.

Adesina ya mutu a watan Fabrairun 2014 bayan ya yi fama da rashin lafiya.

Aisha Buhari na so a dunga damawa da mata a siyasar arewa

A wani labarin, mun ji cewa uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari ta bukaci shugabanni a yankin arewacin Najeriya da su dunga koyi da takwarorinsu na kudu wajen ba mata madafun iko.

Aisha Buhari na so a dunga nada mata a matsayin mataimakan gwamna a jihohin arewa kamar yadda ake yi a kudu musamman a yankin kudu maso yamma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel