Rikicin PDP: Magoya Bayan Atiku A Ribas Sun Aike Wa Wike Sako Mai Ƙarfi

Rikicin PDP: Magoya Bayan Atiku A Ribas Sun Aike Wa Wike Sako Mai Ƙarfi

  • Magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Abubakar Atiku, sun gargadi Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas
  • A wani sako mai karfi da suka tura wa gwamnan na Ribas, magoya bayan Atiku sun dage cewa ba za su durkusa wa Wike a jihar ba
  • Gabanin babban zaben shekarar na 2023, masu biyayya ga Atiku da Gwamna Ifeanyi Okowa sun dage cewa Wike yana son karya lagwon jam'iyyar ne a jihar

Jihar Ribas - Mambobin kwamitin yakin neman zabe na Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, a jihar Ribas sun hada kai sun nuna goyon bayansu baki daya ga Atiku.

Sun bayyana goyon bayansu ga Atiku duk da barazanar kama su umurnin da Gwamna Nyesom Wike ya yi, Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Tashin hankali ga PDP, dangin abokin takararsa sun koma APC, tsagin Tinubu

Wike da Atiku
Rikicin PDP: Magoya Bayan Atiku A Ribas Sun Aike Wa Wike Sako Mai Karfi. Hoto: PDP Governors in Action.
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Direkta Janar na kwamitin a jihar Ribas, Dr Abiye Sekibo ya furta hakan ne a ranar Laraba, 30 ga watan Nuwamba, a taron da suka da kungiyar Atiku Democratic Movement da Concerned Ogoni PDP Elders Council a Fatakwal.

Magoya bayan Atiku sun yi fito na fito da Wike a wani mataki

Tsohon ministan sufurin ya bukaci mazu zabe a jihar su yi watsi da mulkin kama-karya da Gwamna Wike ke yi a jihar kuma su mara wa Atiku Abubakar baya a zaben 2023, rahoton Leadership.

Ya ce:

"Ba za mu bauta wa gunkin gwal da Nebuchadnezzar ya gina a Babylon ba, mune Shedrach, Meshach, da Abednego na wannan zamanin.
"Ya gina gunki na gwal wanda shine kudi kuma ya bukaci mutane su rika bauta masa, su yi duk abin da ya ce. Shedrach, Meshack da Abednego sun ce ba za mu bauta wa gunkin da ka gina ba. Wannan shine matsayar kungiyar Atiku a jihar Ribas. Za su iya yaga fostan Atiku, su kawo dokoki amma muna tare da gaskiya."

Kara karanta wannan

Ku zabi mijina, ya fi Tinubu: Matar Atiku ta fadi dalilan da za su sa Yarbawa su zabi PDP

A bangarensa, mamba na kungiyar kamfen din, Sir Celestine Omehia ya ce an magance rikicin cikin gida na jam'iyyar kuma sun shirya su cigaba.

Atiku ya sake tsokaci kan rikicinsa da Wike, ya ce sun yi gaba

A wani rahoton, Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben shekarar 2023 ya ce tuni sunyi gaba sun dena kula duk wani barazana ga nasararsu a zaben 2023.

A kalla gwamnoni guda 5 ne na PDP ke matsa lamba ga jam'iyyar na cewa sai ta sauke shugabanta na kasa Iyorchia Ayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164