2023: APC Bata Damu Da Makomarku Ba, Atiku Ga Matasan Najeriya
- Gabannin babban zaben 2023, dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya shawarci matasan Najeriya kan wanda yakamata su zaba
- Atiku ya gargadi matasa a kan zaban Bola Tinubu cewa APC bata damu da makomarsu ba
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce ya yiwa matasan Najeriya tanadi na musamman idan har ya gaje Buhari a zabe mai zuwa
Ondo - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya kalubalanci yan Najeriya da su fatattaki jam’iyyar All Progressives Congress (APC), don dawo da kimar kasar.
Musamman tsohon mataimakin shugaban kasar ya fadama matasa da kada su yi kuskuren zaban APC, wacce bata damu da gobensu da iliminsu ba.
Atiku ya bayyana hakan ne yayin gangamin yakin neman zabensa a jihar Ondo, jaridar Vanguard ta rahoto.
Zan ba matasa maza da mata ilimi da tallafi don su dogara da kansu idan na ci zabe, Atiku
Dan takarar shugaban kasar ya kuma sha alwashin ware makudan kudade ga bangaren ilimi, rahoton Channels TV.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Atiku ya ce:
"Mun fara gangamin yakin neman zabe a jihar Ondo a kudu maso yamma kuma da gangan ne, saboda muna so muna nuna mako cewa mun ji dadin abun da kuka yi mana a zaben baya.
"Wannan ne dalilin da yasa idan kuka sake maimaita haka, mun yi alkawarin magance rashin tsaro, za mu tabbatar da ganin cewa duk hanyoyin gwamnatin tarayya da ke sada mutum da jihar Ondo sun zama wanda ababen hawa za su iya bi.
"Za mu tabbatar da ganin cewa matasanmu maza da mata sun samu aiki, za mu ware isasshen kudi don tabbatar da ganin cewa mun baku aiki.
"Wannan ne dalilin da yasa a takardar manufarmu, mun bayyana cewa za mu ware dala biliyan 10 don tabbatar da ganin cewa mun samar da kananan sana'o'i ga maza da mata don su dogara da kansu. Shine babban manufarmu ta daya.
"Za kuma mu samar da isasshen kudi saboda ilimi don jami'o'inmu su ci gaba da aiki da kyau, ba irin wanda muke fuskanta a yau ba. APC bata damu da karatunku ba.
"Kuna iya kwatanta abun da PDP ta yi a shekaru 14 da abun da APC ta yu a shekaru 8, kuma kuke son sake kuskuren zaban APC kuma? Mun ce a'a."
Ku zabi mijina zai dauki nauyin karatunku kyauta, Titi Atiku
A baya mun ji cewa, uwargidar Atiku Abubakar, Misis Titi ta bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da APC sun gaza.
Titi Atiku ta bayyana cewa mijinta Bafulatani ne amma ba makashi ba don haka zai kawo karshen mayakan Boko Haram.
Ta kuma bayar da tabbacin cewa idan suka lashe zabe a 2023, maigidanta zai kula da daukar nauyin karatun al'ummar kasar.
Asali: Legit.ng