Atiku Yaci Zaben 2019, Fashi Aka Yi Masa, Titi Atiku ta Fasa Kwai

Atiku Yaci Zaben 2019, Fashi Aka Yi Masa, Titi Atiku ta Fasa Kwai

  • Uwargidan ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar PDP, Titi Abubakar, ta sanar da cewa fashi aka yi wa mijinta bayan ya ci zaben 2019
  • Titi tace ita diyar jihar Ondo ce kuma tana tsaye gabansu inda take rokonsu da su zabi Atiku saboda ya zama wani bangarensu
  • Gwamna Okowa ya sanar da cewa idan aka zabesu ba za a sake fadawa yajin aiki ba kuma zasu tallafawa matasa yadda ya dace

Akure, Ondo - Titi, Uwargidan Atiku Abubakar, ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar PDP, tace mai gidanta ya ci zaben 2019 na shugabancin kasa da yayi takara, jaridar TheCable ta rahoto.

Matar Atiku Abubakar
Atiku Yaci Zaben 2019, Fashi Aka Yi Masa, Titi Atiku ta Fasa Kwai. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Ta sanar da hakan ne a Akure, jihar Ondo yayin gangamin yakin neman zaben mijinta da taje.

A shekarar 2019, an ayyana Shugaba Buhari wanda ya ci zaben bayan ya lallasa Abubakar, wanda ke bin sa a baya da kusan kuri’u miliyan hudu.

Kara karanta wannan

A Karon Farko Za'a Samu Bayerabiya A Matsayin Mace Lamba Daya Idan Kuka Zabi Atiku, Titi Atiku

Abubakar ya kalubalanci wannan nasarar a kotu amma ya fadi har zuwa kotun koli.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Mutane na, ni diyarku ce gani a gaban ku ina sanar muku cewa mijina yayi a baya. A zaben da ya gabata, mijina ne ya ci amma aka yi amsa fashi.”

- Titi tace.

“Mijina Bafulatani ne amma ba makashi bane kuma a tare muke. Na koyar da shi al’adar mu kuma yanzu wani bangare ne namu.
“A yayin mulkin Obasanjo, Atiku ne ya kawo ire-irensu El-Rufai, Ngozi Okonjo da sauransu da suka yi aiki da kyau a Najeriya.”

A yayin jawabi a ralin, Abubakar ta dora laifin tabarbarewar harkar ilimi a kasar nan kan gwamnatin APC.

Ifeanyi Okowa, Gwamnan jihar Delta da ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa na PDP, yace idan aka zabesu, Gwamnatin PDP zata mayar da hankali kan matasa kuma babu jami’a da zata tafi yajin aiki.

Kara karanta wannan

Abinda 'Yan Siyasar Mu Na Arewa Zasu Koya Daga 'Yan Kudu, Aisha Buhari

“A watanni takwas da suka gabata, matasa suna gida kuma hakan bai dace ba. Atiku ya samar da dabarun tabbatar da cewa babu jami’ar da ta tafi yajin aiki saboda za a mayar da hankali kan matasan kasan, tare da saka ajiye kudin taimakawa matasa wadanda zasu so shiga harkar kasuwanci.”

- Okowa yace.

“Matukar kun zabi Atiku, yunwa da rashin aikin yi zai zama tarihi.”

An kai wa tawagar kamfen din Atiku farmaki a Kaduna

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto muku cewa wasu bata gari sun kai wa tawagar kamfen din Atiku Abubakar farmaki a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng