NNPP Ba Za ta Sa Hannu a Yarjejeniyar Zaman Lafiya ba, Sai An Kamo Shugaban APC

NNPP Ba Za ta Sa Hannu a Yarjejeniyar Zaman Lafiya ba, Sai An Kamo Shugaban APC

  • Idan ba a gyara ba, Abba Kabir Yusuf ba zai rattaba hannunsa a wajen yarjejeniyar zaman lafiya ba
  • Abba Gida-Gida yana so a kama Shugaban APC na Kano watau Abdullahi Abbas domin a hukunta shi
  • A ala’ada ana sa hannu tsakanin ‘yan takara, jam’iyyar NNPP ta turje, tacer dole a ja kunnen APC

Kano - Abba Kabir Yusuf mai neman zama Gwamnan jihar Kano a karkashin jam’iyyar NNPP yana barazanar kauracewa yarjejeniyar zaman lafiya.

A rahoton Daily Trust na ranar Talata, an ji cewa Injiniya Abba Kabir Yusuf ba zai je wajen taron sa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya a zaben 2023 ba.

‘Dan takaran yace babu ruwan shi da wannan maganar, muddin ba a kamo shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas domin ayi masa hukunci ba.

A wani jawabi da ya fitar ta bakin Mai magana da yawunsa, Sanusi Bature, ‘dan takaran NNPP ya maidawa Abbas martanin maganganun da ya yi.

Sai an koma Abdullahi Abbas

Abba Gida Gida yana zargin shugaban na APC da kawo tashin-tashina, yake cewa idan ba a koyawa Abbas hankali ba, ba zai je taron zaman lafiya ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abba K. Yusuf yace yaron Abdullahi Abbas ya jagoranci ta’adin da aka yi, inda aka raunata wasu daga cikin magoya bayan jam’iyyaar NNPP da ke jihar.Ya kamata a cafke 'Yan NNPP - APC

Ana hakan kuma sai ga jam’iyyar APC tana kira ga jami’an tsaro da su cafke jiga-jigan NNPP na Kano bisa zarginsu da hannu a hare-haren da aka kai.

Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben APC, Muhammad Garba yace 'Yan NNPP ne suka tada rikici da suka je daurin aure a yankin Gwale.

Garba ya kara da cewa, abin takaici ne ‘dan takarar na NNPP mai hamayya ya dora laifin rikicin siyasar Kano ga APC, har da cewa ayi ram da Shugaban ta.

NNPP ta shiryawa 'Dan Sarki

Aminiya tace shi ma Shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, Umar Haruna Doguwa, ya nuna za su kauracewa yarjejeniyar zaman lafiyar idan aka tafi a haka.

Doguwa yayi raddi ga Abdullahi Abbas, yana fada masa sun shiryawa duk tsiyar da yake ji da ita, amma Abbas ya fito yace an yi masa mummunar fassara.

Akwai matsala a NNNP a Kaduna

Wani ‘Dan takaran Majalisa ya bayyana cewa Sulaiman Hukunyi zai kashewa ‘Yan jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP kasuwa a jihar Kaduna.

Wasu sun ce idan da hali a canza ‘dan takaran Gwamnan Kaduna a 2023, idan ba haka ba zai yi wahala jam’iyya mai kayan dadi ta kai labari a zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel