Yanzu Yanzu: An Kama Tsohon Minista Da Wasu Mutane Kan Zargin Lalata Kayan APC
- Ana zargin yan sanda sun kama Ikrah Aliyu Bilbis, tsohon karamin ministan labarai a jihar Zamfara
- An cafke Bilbis wanda ya kasancve dan takarar kujerar sanata na jam’iyyar PDP tare da wasu kan aikata barna
- Rahotanni sun kawo cewa ya lalata wasu allunan yakin neman zaben jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne a jihar
Zamfara - Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta kama tsohon karamin ministan labarai kuma dan takarar kujerar sanata na PDP a zaben 2023, Ikrah Aliyu Bilbis.
Yan sandan sun cafke Bilbis da wasu mutane kan zargin farfasa allunan yakin neman zabe mallakin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
An zargi gwamnatin APC a jihar Zamfara da kama 'ya'yan PDP
Da yake zantawa da manema labarai a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, jigon PDP, Aliyu Adamu Barmo, ya nuna damuwa kan yadda ake kama mambonin PDP, jaridar Leadership ta rahoto.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa ana kame su ne saboda ziyarar da tsohon dan takarar gwamnan babbar jam’iyyar adawar, Dauda Lawan Dare ya kai jihar.
Barmo ya ce wannan hukunci da gwamnatin APC ta dauka na amfani da yan sanda kan jiga-jigan PDP ba daidai bane.
Ya kuma jadadda cewar ziyarar da Dauda Lawan Dare ya kawo mahaifarsa yana kan daidai saboda yana da yanci.
Daily Post ta rahoto cewa sakataren jam’iyyar PDP, Alhaji Muhammad Abdullahi Zangina, ya tabbatar da kamun yana mai cewa baya rasa nasaba da zargin da APC tayi na cewa an farfasa mata allunan kamfen.
Har ila yau da yake martani kan lamarin, mukaddashin shugaban PDP a jihar Mukhtar Lugga, ya yi Allah wadai da kamun mambobin PDP da gwamnatin jihar ke yi.
Ya bayyana cewa gangamin PDP da aka yi a ranar Lahadi, an yi sa ne bisa yardar hukumomin da suka dace.
Martanin yan sanda
Da aka tuntube shi, kakakin rundunar yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya ki amsa kiraye-kirayen waya da sakonnin tes da aka tura masa.
APC za ta sake darewa kujerar shugabancin kasa a 2023, jigon jam'iyyar
A wani labari na daban, jigon jam'iyyar APC mai mulki ya nuna karfin gwiwar cewa za su kai labari a babban zaben 2023 mai zuwa domin a cewarsa yan Najeriya za su sake zabansu.
Bala Ibrahim ya yi ikirarin cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta mayar da yan Najeriya da dama sun zama attajirai wanda ba a taba irin haka ba a tarihin kasar.
Asali: Legit.ng