2023: Gwamna Zulum Ya Sha Alwashin Hana ‘Yan Adawa Samun Nasarar Komai a Borno

2023: Gwamna Zulum Ya Sha Alwashin Hana ‘Yan Adawa Samun Nasarar Komai a Borno

  • Farfesa Babagana Umara Zulum ya kaddamar da kwamitin da za suyi wa APC aikin kamfe a Borno
  • Gwamnan ya bukaci ‘yan kwamitin su dage wajen ganin jam’iyyar APC ta doke kowa a zaben 2023
  • Zulum ya bada hakuri ga Atiku Abubakar a kan harin wasu bata-gari suka kai wa tawagarsa kwanaki

Borno - Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya sha alwashin ganin jam’iyyar APC ta lashe duk wani zabe da za a shirya a shekarar 2023.

Babagana Umara Zulum yana so a hana jam’iyyun adawa lashe ko da a rumfa daya ne a fadin jihar Borno a mulkinsa, Vanguard ce ta fitar da rahoton nan.

Mai girma Gwamnan ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya hadu da magoya baya da masu ruwa da tsaki wajen kaddamar da kwamitin yakin zaben APC.

Kara karanta wannan

LP Ta Batawa Atiku Lissafi, Shugaban PDP Yana Goyon Bayan a Zabi Peter Obi

Jam’iyyar APC ta reshen jihar Borno, ta rantsar da mutum 800 da za suyi mata yakin zabe. An kaddamar da ‘yan kwamitin a gidan gwamnati na Maiduguri.

An rahoto Gwamnan yana cewa abin dariya ne an samu wasu sun lallabo a karkashin jam’iyyar PDP da ta mutu, suna neman mutane su zabe su.

Farfesa Babagana Zulum ya zargi ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP da jawo rigima da sunan yin kamfe. An ji shi a shafinsa yana cewa ya cika alkawarin da yayi a 2019.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Zulum
Gwamna Babagana Umara Zulum Hoto: @GovBorno
Asali: Twitter

An ba Atiku hakuri

The Nation tace Gwamnan ya yi amfani da damar wajen bada hakuri ga Atiku Abubakar, a dalilin harin da tsageru suka kai wa tawagarsa wajen kamfe.

A jawabin da ya gabatar a jiya, Farfesa Babagana Zulum ya tunawa ‘yan adawa cewa Borno jihar APC ce, la’akari da irin abubuwan da ya yi a cikin shekaru uku.

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Kaddamar da Gangamin Kamfen din APC a Gaya

Duk da haka, Farfesan yace jam’iyyar APC ba ta tsoron wata jam’iyyar adawa da ke neman zabe.

Zulum yana tunkaho da cewa gwamnatinsa ta bunkasa harkar tsaro, ta kawo ayyukan yi, ta tallafawa matasa, kuma an maida mutane garuruwansu.

Shugaban APC na Borno, Alhaji Ali Dalori ya yabi Gwamnan amma ya nuna bai ji dadin rashin halartar Hon. Muktari Aliyu Betara wajen rantsarwar ba.

Abin da nake so in bari - Muhammadu Buhari

Ganin cewa nan da watanni shida zai bar gadon-mulki, an ji labari cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya yi bayanin babban burin da yake da shi a rai,

Buhari ya yi jawabi na musamman a taron ECOWAS, yace zai dage wajen ganin an yi zabe na gaskiya da gaskiya a Kasashen yammacin nahiyar Afrika.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng