LP Ta Batawa Atiku Lissafi, Shugaban PDP Yana Goyon Bayan a Zabi Peter Obi
- Takarar Peter Obi ta samu goyon bayan wani babban jigo na jam’iyyar hamayya ta PDP da ke kasar waje
- Mike Okoli yace babu ‘dan takaran da ya cancanta a zaba a shekara mai zuwa irin Peter Obi na jam’iyyar LP
- Dr Okoli bai goyon bayan tikitin APC na Musulmi da Musulmi da kuma tsaida ‘Dan Arewa da aka yi a PDP
FCT, Abuja – Shugaban jam’iyyar PDP a kasar Rasha kuma jagoran mutanen Najeriya a kasar wajen, yana goyon bayan takarar Peter Obi a zaben 2023.
Legit.ng ta rahoto cewa Dr. Maurice Okoli yana ganin cewa Peter Obi mai neman shugabancin kasar nan a jam’iyyar LP, ya fi cancanta ya karbi mulki.
Maurice Okoli yace Obi ya sha ban-bam da sauran ‘yan takaran shugaban kasa, bai da makusa.
Babban mai binciken a sashen nazarin Afrika a wata cibiya da ke kasar Rasha, ya yi kira ga mutanen Najeriya su zabi tsohon Gwamnan na jihar Anambra.
Mutane sun farga yanzu
Shugaban kamfanin Markol Group Russia yana tallata Obi a lokacin da Alhaji Atiku Abubakar yake harin zama shugaban Najeriya a jam’iyyarsu ta PDP.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewar Okoli, ‘dan takaran jam’iyyar hamayyar ta LP ya zaburar da al’umma, kuma matasa sun yi amanna da cewa shi ne zai iya kawo gyara a Najeriya.
Bugu da kari, shugaban na jam’iyyar PDP ya zage da cewa Obi ya yi abin a yaba a lokacin da ya yi Gwamna, don haka zai iya kawo gyaran da ake buri.
Masu mulki suyi hattara - Okoli
A jawabin da Dr. Okoli ya fitar, ya yi barazanar cewa muddin masu rike da madafan iko suka hana Obi karbar mulki ta hanyar magudi, ba za a zauna lafiya ba.
Masanin yake cewa ya kamata wadanda ke kan mulki su fahimci cewa an kama hanyar yin juyin-juya hali a Najeriya, don haka ya zama dole suyi hattara.
Vanguard tace Okoli ya soki tikitin Musulmi da Musulmi da APC tayi, sannan yace PDP tayi kuskuren tsaida Musulmin Arewa bayan Muhammadu Buhari.
APC ta shiga Kudu maso kudu
A taron siyasan da jam’iyyar APC ta shirya a Kudu maso Kudancin Najeriya, an samu rahoto cewa Zahra Buhari-Indimi ce ta wakilci Aisha Buhari a garin Kalaba.
Sanata Remi Tinubu da ‘yan tawagar ta sun ziyarci fadar Mai martaba Edidem Ekpo Okon Abasi Otu V, kuma sun nemi goyon bayan mata da matasan Kuros Riba.
Asali: Legit.ng