Shugabar Matan APC Ta Kasa Ta Yi Alkawarin Hadawa Tinubu Kuri'u Miliyan 40 a 2023

Shugabar Matan APC Ta Kasa Ta Yi Alkawarin Hadawa Tinubu Kuri'u Miliyan 40 a 2023

  • Shugabar matan APC ta ƙasa, Betta Edu, ta sha alwashin haɗa wa Bola Tinubu kuri'u 40 na matasa da mata a zaɓen 2023
  • Misis Edu tace gwamnatin Bola Tinubu da Shettima zata sa bukatun mata a gaba kamar yadda suka yi a jihohinsu
  • Matar Tinubu ta roki mahalarta gangamin a Kalaba jihar Kuros Riba ta roki kowa ya karbi PVC su zabi APC a 2023

Calabar, Cross River - Shugabar matan jam'iyyar APC ta ƙasa, Betta Edu, ta kudiri aniyar tara wa dan takarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, kuri'u miliyan 40 a babban zaɓen 2023.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Edu ta ɗauki wannan alƙawarin ne a Kalaba, babban birnin jihar Kuros Riba a wurin gangamin mata da matasa na kudu maso kudu.

Kara karanta wannan

"Mazi Tinubu": Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam'iyyar APC Ya Samu Sarauata A Yankin Su Peter Obi

Betta Edu.
Shugabar Matan APC Ta Kasa Ta Yi Alkawarin Hadawa Tinubu Kuri'u Miliyan 40 a 2023 Hoto: Betta Edu
Asali: UGC

Tace ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar APC da abokin takararsa, Kashim Shettima, sun zuba wa al'umma aiki lokacin suna matsayin gwamna a jihohinsu.

A cewar Misis Edu, rawar da suka taka a jihohinsu ta kai a sake basu dama su kara yi wa al'ummar Najeriya aiki a matakin ƙasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ɗan takarar shugaban ƙasa na APC babban mai son ci gaban mata da matasa ne don haka ya cancanci samun tulin goyon baya da kuri'unsu. Tinubu ya taimaka wa mata kuma mun gani a ƙasa."
"Ya goyi bayan matarsa wacce take Kirista har ta kai matsayin Sanata da wasu mata a jiharsa (Legas). Idan kuka koma jihohinku, ku shiga lungu da sako ku tattara wa APC masoyan da zasu zaɓi Tinubu/Shettima."
"Ku tabbata kun karbi Katin zabenku sannan ku garzaya runfunan zaɓenku ku dangwalawa Bola Tinubu a watan Fabrairu, 2023."

Kara karanta wannan

2023: Atiku da Tinubu Sun Kara Shiri, Sun Yi Sabbin Naɗe-Naɗe a Kwamitin Yakin Neman Zabe

- Betta Edu.

Mata zasu amfana idan Tinubu ya ci zabe - Oluremi Tinubu

A nata jawabin, Oluremi Tinubu, mai ɗakin dan takarar shugaban ƙasa na APC, ta roki matan kudu maso kudu a babban zaɓen 2023 saboda zasu amfana sosai a mulkin mijinta.

"Mun shirya ba mata muhimmanci a gwamnatin gaba da izinin Allah, zaben Tinubu/Shettima zaɓi ne na cigaba, zata buɗe wa matasa su samu dama kuma ta dawo da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa."

Haka zalika mai ɗakin gwamna Ben Ayade na jihar Kuros Riba, Linda Ayade, ta roƙi mazauna jihar su mallaki katin zaɓe kuma su dangwalawa APC a zaɓen watan Fabrairu mai zuwa.

A wani labarin kuma Jam'iyar APC da Ɗan Takarar shugaban ƙasa sun samu gagarumin goyon bayan daga ƙungiyoyi 10

Wasu ƙungiyoyin da suka kwashe shekaru suna tare da Atiku Abubakar na PDP, sun ce sun gaji, sun koma jam'iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Karar da Aka Shigar da Bola Tinubu Na APC

Da yake karbansu a hukumance, gwamna Bello Matawalle na Zamfara ya umarci a sanya su cikin kwamitin kamfe, ya bukaci su yi amfani da kwarewarsu don APC ta samu nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262