Rade-Radin Shiga Shi’a: Jarumin Barkwanci Ali Madagwal ya Magantu

Rade-Radin Shiga Shi’a: Jarumin Barkwanci Ali Madagwal ya Magantu

  • Jarumin barkwanci a masana’antar Kannywood, Aliyu Muhammad Idris wanda aka fi sani da Ali Artwork ko Madagwal, ya musanta rade-radin da ake yi na cewa ya shiga shi’a
  • Madagwal ya sanar da cewa ya saba kai ziyara wurin malumman izala, Tijjaniya da Kadiriyya duba da yanayin sana’arsa ta nishadantarwa wacce ke birge kowa
  • Ya sanar da cewa Sheikh Zakzaky ya bashi muhimman sako don ya isarwa abokan sana’arsa na Kannywood tare da nasihohi kan yadda suke tafiyar da lamurransu

FCT, Abuja - Fitaccen jarumin barkwanci Aliyu Muhammad Idris wanda yafi shuhura da Madagwal, ya sanar da cewa jagoran kungiyar Shi’a, Sheikh Ibrahmi Zakzaky ya bashi muhimman sako ya isarwa da ‘yan Kannywood.

Ali Artwork da Sheikh Ibrahim Zakzaky
Rade-Radin Shiga Shi’a: Jarumin Barkwanci Ali Madagwal ya Magantu. Hoto daga fimmagazine.ng
Asali: UGC

Jarumin ya musanta rade-radin da ake yadawa kan ya karbi shi’a shiyasa ya kai wa malamin ziyara har gidansa na Abuja.

Kara karanta wannan

Hotuna Daga Shagalin Bikin Jarumar Kannywood, Halima Atete, Jama'a Sun Yi Martani

A zantawa da yayi da mujallar Fim, Madagwal yace:

“Duk masu cewa na karba shi’a karya suke yi. Wanda duk ya san ni, ya san a kowacce darika ina da jama’a. Na saba ziyartar malamai tuntuni. Malaman Izala, Tijjaniya, Kadiriyya da sauran malamai duba da tsarin sana’a ta ta nishadantarwa. A kowanne bangaren al’umma ana ji na kuma ana kallo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Hakazalika, jama’a da yawa suna so kuma ina birge su kan abinda nake yi. Suna kuma son mu kulla mu’amala koda ta kasuwanci ce ko wani abu mai kyau. Zuwa na wurinsa ba sabon abu bane.”

Ya kara da cewa:

“Na taba ziyartar Sheikh Gumi kuma mun yi hira da shi kan batun zakka da wakafi.
“Na taba ziyartar ‘dan Sheikh Dahiru Bauchi kuma yi yi maganganu.
“Har ila yau, Sheikh Zakzaky ma mun kai masa ziyarar sada zumunta tare da yi masa jaje da sauransu.”

Kara karanta wannan

Babban Malami a Najeriya Ya Umarci Mabiyansa Karsu Zabi Jam'iyyar APC a 2023, Ya Fadi Hujjarsa

Ali ya kara da cewa:

“Daga cikin mutanensa akwai masu so na, suna kallon nishadantarwa da nake yi da sauransu. Wannan shi ne dalilin zuwa na.”

Abinda muka tattauna

Mujallar Fim ta rahoto cewa, Madagwal ya bayyana cewa ya ji dadin tattaunawa da Malam kuma ya ganar dasu wasu lamurran rayuwa da basu sani ba. Ya kuma basu shawarwari kan sana’arsu da yadda wasu jama’a ke kallonsu matsayin masu bata tarbiya.

“Wannan abu ne da bai kamata ba kuma harka ce da za a iya amfani da ita wajen aike sako, mu yi da kyau kuma kada mu yi abinda zai zubda kimar mu ko ta addininmu. Mu dinga nunawa mutane yadda zasu yi rayuwa mai kyau.
“Malam ya bamu shawara tare da nuna cewa sukar da muke sha a harkar duk ba haka bace.
“Ya kara da bayyana mana muhimman abubuwa da za mu dinga amfani dasu wurin wayar da kan mutane tunda harkar mu mai tsohon tarihi ce.”

Kara karanta wannan

Binciken ‘Yan Sanda Ya Nuna Jihohi 2 da Za a fi Samun Tashin Hankali a Zaben 2023

- Ali ya kara da cewa.

Jaruma Halima Atete zata Amarce

A wani labari na daban, Legit.ng ta kawo muku cewa jarumar Kannywood Halima Atete zata yi aure.

Zata auri Mohammed Mohammed Kala a ranar 26 ga watan Nuwamba a Maiduguri dake jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Online view pixel