Yanzu-yanzu: Buhari ya nada sabon shugaban ma'aikatan fadarsa

Yanzu-yanzu: Buhari ya nada sabon shugaban ma'aikatan fadarsa

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin shugaban ma'aikatan fadarsa

- Farfesa Ibrahim Gambari dan asalin jihar Kwara ne kuma tsohon sakataren majalisar dinkin duniya ne

- Farfesan mai shekaru 78 a duniya ya taba zama ministan harkokin waje a Najeriya tsakanin 1984 zuwa 1985

Tsohon sakataren majalisar dinkin duniya, Farfesa Ibrahim Gambari ya zama magajin marigayi Abba Kyari.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada tsohon sakataren majalisar dinkin duniyan a matsayin shugaban ma'aikatan fadar sa.

Gambari dan asalin jihar Kwara ne kuma ya yi tsohon ministan harkokin waje tsakanin 1984 zuwa 1985.

Farfesan na da babbar shaidar kwarewa da jajircewa. Yana da shekaru 78 a duniya a yanzu da ya maye gurbin marigayi Abba Kyari.

Farfesa Gambari ya yi aiki tukuru a yayin da yake sakataren majalisar dinkin duniya, kuma mai bada shawara na musamman ga babban sakataren nahiyar Afrika tsakanin 1999 zuwa 2005.

Mutum ne sananne a gida da wajen kasar nan.

Shine shugaban majalisar zartarwa ta jami'ar jihar Kwara a halin yanzu.

Yanzu-yanzu: Buhari ya nada sabon shugaban ma'aikatan fadarsa
Yanzu-yanzu: Buhari ya nada sabon shugaban ma'aikatan fadarsa. Hoto daga ThisDay
Asali: Twitter

KU KARANTA: COVID-19: Jerin jihohi 6 da WHO za ta gwada maganin korona a Najeriya

A wani labari na daban, gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce jihohin Legas, Abuja, Ogun, Kaduna, Sokoto da Kano ne kungiyar kiwon lafiya ta duniya za ta gwada maganin cutar korona a kan mutanen ta, SaharaReporters ta wallafa.

Gwajin maganin, wanda gwajin ingancin maganin ne na duniya na daga cikin kokarin kungiyar kiwon lafiyan na samar da magani da kuma riga-kafin korona a cikin kankanin lokaci.

Ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire ne ya sanar da hakan a ranar Litinin a Abuja yayin jawabi a kan inda kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da korona suka kwana.

Ehanire ya ce zuwa ranar Lahadi, kasar nan ta kara gwajin samfur 1,127 inda jimillar gwajin da aka yi ya kai 27,078. 4,399 daga ciki kuwa duk suna dauke da cutar daga jihohi 35 na kasar nan. Kashi 70 bisa dari duk maza ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel