Zaben 2023: Dan Takarar Gwamna Mai Karfi A Jihar Arewa Ya Bayyana Shirinsa Na Karbe Mulki Daga Hannun APC

Zaben 2023: Dan Takarar Gwamna Mai Karfi A Jihar Arewa Ya Bayyana Shirinsa Na Karbe Mulki Daga Hannun APC

  • An fada wa dalibai da suka dena zuwa makaranta a Kaduna cewa za su koma makaranta
  • Dan takarar kujerar gwamna na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, Isa Ashiru, ya yi wa mutane wannan alkawarin
  • Ya ce gwamnatinsa za ta bada muhimmanci a bangaren ilimi musamman kimiyya da fasaha

Kaduna, Kaduna - Isa Ashiru, dan takarar gwamna na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a jihar Kaduna, ya sha alwashin sake tsarin makarantun gwamnati a jihar idan an zabe shi gwamna a zaben 2023.

Ashiru ya yi wannan alkawarin ne yayin wani taro tare da kungiyar yan jarida na kasa, NUJ, reshen jihar Kaduna, Radio Nigeria ta rahoto.

Isa Ashiru
Zaben 2023: Dan Takarar Gwamna Mai Karfi A Jihar Arewa Ya Bayyana Shirinsa Na Karbe Mulki Daga Hannun APC. Hoto: Isa Ashiru Kudan.
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Allah Raka Taki Gona, APC Ta Maida Martani Ga Tsohon Sakataren Buhari Da Ya Zabi Goyon Bayan Atiku

Yayin da ya ke bayyana damuwarsa kan abin da ke faruwa, dan takarar na PDP ya bayyana cewa tsadar kudin makaranta a jihar ya janyo mutane da dama sun dena zuwa makaranta.

Ya bayyana cewa iyaye da dama sun cire yaransa daga makaranta saboda tsadar kudin makarantar a irin wannan halin matsalin tattalin arziki.

Nigerian Tribune ta ambato Ashiru yana cewa:

"Za mu kafa kwamiti da zai bada shawarwarin hanyoyin yadda iyayen da suka cire yaransu daga makaranta za su mayar da su."

Dan takarar na PDP ya ce ilimi na da muhimmin rawa wurin cigaban al'umma kuma al'umma masu ilimi ne kawai za su iya cigaba.

Amma, ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta bawa ilimi muhimmanci musamman kimiyya da fasaha a matakin sakandare da gaba da sakandare.

Zaben 2023: Ashiru ya yi alkawarin rage bashin da ake bin Kaduna

Hakazalika, Ashiru ya koka kan karuwar bashi da ake bin jihar da ya ce an karbo a cikin gida da kasashen waje.

Kara karanta wannan

Fasto Ya Ja Kaya: Wani Shugaban Majami'a Ya Dirkawa Mambobinsa Mata 20 Ciki

Ya ce gwamnatinsa za ta yi aiki don ganin ta rage bashi a jihar.

Da ta magana wurin taron, Shugaban NUJ a Kaduna, Asma'u Halilu, ta ce an shirya taron ne don bawa yan takarar damar fada wa mutanen jihar shirye-shiryensu da dalilin da yasa za a zabe su.

Ta ce yan jarida ne idon al'umma, kuma za su cigaba da habbaka mulki mai kyau da bin dokoki.

Isa Ashiru: Abu 3 Da Zan Mayar Da Hankali A Kai Idan Na Zama Gwamnan Kaduna

Dan takarar gwamna na PDP a jihar Kaduna, Isa Ashiru Kudan, ya bayyana abubuwa uku da za mayar da hankali kansu idan ya zama gwamna.

BBC ta rahoto cewa Ashiru Kudan, wanda ke takarar Kaduna karo na uku ya ce abin farko da zai mayar da hankali kai shine tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel