Zan ‘Sake Cajin’ Tafkin Chadi Idan Aka Zabe ni, Tinubu ya Sake Subul da Baka
- ‘Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa zai ‘sake cajin’ tafkin Chadi idan aka zabe shi
- Tinubu ya sanar da cewa, Buhari na yawan bayyana damuwarsa kan yunwa da matsalar ta’addanci idan suna tare, don haka zai shawo kan su
- Tinubu yayi alkawarin cewa zai shawo kan matsalar Mambila da kuma wutar lantarki wacce yace take cin tuwo a kwarya ga kasar nan baki daya
Alkaleri, Bauchi - ‘Dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a ranar Laraba ya tabbatarwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa zai shawo kan matsalolin tafkin Chadi idan ya zama shugaban kasa.
Channels TV ta rahoto cewa, a yayin jawabi a wurin kaddamar da aikin Kolmani na hakar man fetur karo na farko a arewacin Najeriya, Tinubu ya sake jaddada cewa zai shawo kan yunwa da ta’addanci.
“A duk lokacin da muka zanta da kai (Buhari), abinda yafi ci maka tuwo a kwarya shi ne batun yunwa da ta’addanci, kana magana kan tafkin Chadi. Bari in tabbatar maka, idan aka zabe ni matsayin shugaban kasa zan sake cajin tafkin Chadi. Kana yawan magana kan Mambila da matsalar wutar lantarki da muke da ita.”
- Tsohon Gwamnan ya sanarwa shugaban kasa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya yabawa Buhari kan yadda ya tsaya tare da jajircewa kan lamurran kasar nan.
“Kai ba mutum bane dake tunanin baya ta hanyar tuna tarihi maras dadi da rashin sa’a, a koda yaushe gaba ku ke kallo.”
- Yace.
Sabunta burin ‘yan Najeriya
Jaridar Punch ta rahoto cewa, ya kara da cewa zai cigaba kamar yadda Buhari yake da hanzari.
“Shiyasa yayin da muke mahawara, na jaddada cewa abinda zamu tattauna a kai shi ne ‘Sabunta buri’ ba tare da na san yau zata zo ba, kuma gashi Yau tana faruwa. Wannan sabunta buri ne ga dukkan ‘yan Najeriya.
“Bari in tabbatar muku cewa zan cigaba da rike cewa zamu sabunta buri kuma mu cigaba daga inda aka tsaya.”
- ‘Dan takarar shugaban kasan na APC ya sanar.
Buhari ya kaddamar da Kolmani Integrated Development Project a yankin Arewa maso gabas a ranar Talata, na farko irin shi a yankin.
Baya ga Tinubu, sauran jiga-jigan da suka halarci wurin suna hada da karamin ministan man fetur, Timipre Slyva da shugaban NNPC, Mele Kyari.
Sauran sun hada da Gwamna Baka Mohammed na jihar Bauchi, Inuwa Yahaya na jihar Gombe, Simon Lalong na jihar Filato.
Tinubu yayi surkulle a KadInvest
A wani labari na daban, Bola Ahmed Tinubu yayi surkulle maras ma’ana a yain da yaje taron KadInvest.
Ya bayyana cewa, Gwamna ElRufai na jihar Kaduna ya gyara rubabben al’amari zuwa lalatacce.
Asali: Legit.ng