Jama’a Sun Yi Martani Bayan Ganin Bidiyon Surkulle da Tinubu Yayi Kan El-Rufai a KadInvest

Jama’a Sun Yi Martani Bayan Ganin Bidiyon Surkulle da Tinubu Yayi Kan El-Rufai a KadInvest

  • Jama’a sun dinga cece-kuce kan surkullen da Bola Tinubu yayi a taron tattalin arziki da zuba hannayen jari na jihar Kaduna karo na bakwai da ya halarta
  • ‘Dan takarar kujerar shugabancin kasan na jam’iyyar APC, yace Nasir El-Rufai ya mayar da rubabben al’amari zuwa lalatacce
  • Kungiyar kamfen din Tinubu ta yi martani inda tace shirmen da Tinubu yayi subul da baka ne wanda kowanne ‘Dan Adam na iya yin shi har da manyan shugabanni

Kaduna - Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ‘dan takarar kujerar shugabancin kasa na jam’iyyar APC yayi surkulle tare da shirme yayin da yake magana kan Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna a jawabin da yayi a taron tattalin arziki da zuba hannayen jari na jihar Kaduna karo na bakwai da ya halarta.

Kara karanta wannan

Abinda Yasa Nake Da Gwarin Guiwar Cewa Ni Zan Lashe Zaben Shugaban Kasa a 2023, Tinubu Ya Magantu

Tinubu da El-Rufai
Jama’a Sun Yi Martani Bayan Ganin Bidiyon Surkulle da Tinubu Yayi Kan El-Rufai a KadInvest. Hoto daga Governor of Kaduna
Asali: Facebook

A yayin jawabi a taron a ranar Asabar, 15 ga watan Oktoban 2022, Tinubu yace Gwamnan Kaduna ya sauya:

“Rubabben al’amari zuwa lalatacce.”
“A bayyane nake rokon Gwamna El-Rufai da kada ya tafi neman karin digiri ko digirin digirgir da sauransu.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

- Tsohon Gwamnan Legas din yace.

“Ba zamu bar ka ka tsere ba. Hangen nesanka, kirkire-kirkirenka da jajircewarka sun sauya rubabbun al’amura zuwa lalatattu wadanda suka zama dole a irin wannan lokacin kuma hakan yasa muka halarci wurin nan.”

Surkullen Tinubu a Kaduna ya tayar da kura

Captain Barbossa, @efa101 yace:

“Shin sai mun zauna mun lura ne ko kuwa? Don a gaskiya har yanzu ban fahimta ba.”

Franklin Omani, @frvnklin yace:

“Mayar da rubabbun al’amura zuwa lalatattu. ‘Yan uwa kada mu yi burus da irin wadannan alamun.”

Kara karanta wannan

Yadda Zan Tsaya Na Yaki Yan Bindiga Idan Na Zama Shugaban Kasa a 2023, Tinubu

Oke Umurhohwo, @OkeStalyf yace:

“Ku kwatanta Tinubu ya wakilci Najeriya a majalisar dinkin duniya. Oh Allah na.”

Alexander, @AlexOgunsina yace:

“Kawai a lokacin da nake tunanin zai yi jawabi mai hankali. Boom ya leaf da.”

HenryAjis, @HenryAjis yace:

“Ko dai kunne na ke min ciwo ne? Mayar da rubabben lamari zuwa lalatacce. Oh ni.”

Sanusi II ya Sanar da Tinubu Cewa Bashi da Jam’iyyar Siyasa, Najeriya ce a Gabansa

A wani labari na daban, tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya, Sanusi Lamido Sanusi a ranar Asabar, ya sanar da ‘Dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu cewa bashi da jam’iyyar siyasa.

Channels TV ta rahoto cewa, Sanusi yayi wannan batun a Kaduna yayin da ake gudanar da taron shekara shekara na KadInvest wanda Cibiyar Habaka zuba Hannayen jari na jihar Kaduna ke shiryawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel