Zaben 2023: Shin Atiku Zai Yi Sulhu Da Boko Haram? Ɗan Takarar Na PDP Ya Bayyana Abinda Ke Zuciyarsa

Zaben 2023: Shin Atiku Zai Yi Sulhu Da Boko Haram? Ɗan Takarar Na PDP Ya Bayyana Abinda Ke Zuciyarsa

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya sha alwashin kawar da Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya
  • Ya bayyana hakan ne yayin kamfen dinsa na shugaban kasa na jihar Gombe a ranar Litinin 21 ga watan Nuwamba
  • Atiku kuma ya yi alkwarin farfado da wutar lantarki don bukasa harkar kasuwanci a jihar

Gombe, Gombe - Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ya bayyana ainihin abin da zai yi wa kungiyar yan ta'adda na Boko Haram.

A wurin kamfen din shugaban kasa na PDP a Gombe a ranar Litinin, 20 ga watan Nuwamba, Atiku ya bayyana shirinsa na kawar da kungiyar yan ta'addan idan ya zama shugaban kasa.

Atiku Abubakar
Zaben 2023: Shin Atiku Zai Yi Sulhu Da Boko Haram? Ɗan Takarar Na PDP Ya Bayyana Abinda Ke Zuciyarsa. Atiku Abubakar.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Shugabbanin Kudu Sun Koka Kan Yadda Aka Maida su saniyar Ware Musamman A Faggen Shugabancin

Dan siyasan, haifafan jihar Adamawa ya ce gwamnatinsa za ta samar da yanayi mai kyau inda kasuwanci za su bunkasa, Vanguard ta rahoto.

Ya fada wa magoya bayansa na jihar Gombe cewa zai farfado da tattalin arzikin Najeriya ta yadda zai bunkasa a idon duniya kamar yadda ya kamata a ce ya faru lokaci mai tsawo.

Atiku ya ce:

"Alkawarin da zan yi a nan Gombe shine tabbatar da cewa mun basu yan kasuwa tallafin kafa masana'antu da za su bawa dukkanku maza da mata ayyukan yi."

Tsohon mataimakin shugaban kasar kuma ya yi magana kan batun lantarki, yana mai cewa ana bukatar lantarki kafin kasuwanci ta bunkasa, ya ce gwamnatinsa na da niyyar farfado da lantarki don taimakawa kasuwanci su cigaba a Najeriya.

Ya ce:

"Idan za a iya tunawa PDP ce ta gina dam din Dakin-Kowa don samarwa arewa maso gabas lantarki da bawa manoma damar yin noma, zan samar da ayyuka da arziki a jihar Gombe idan kuka bani kuri'unku."

Kara karanta wannan

Gara in Mutu da dai in Gazawa Magoya Bayana, Peter Obi

"Na yi alkawarin idan kuka zabe ni, abin da muka fara, zan tabbatar an samar da lantarki daga dam din Dakin-Kowa da zai isa dukkan arewa maso gabas.
"Zan inganta noma saboda manoman mu su samu damar yin noman damina da rani."

Atiku ya yi magana kan kawar da ta'addanci

Hakazalika, Atiku ya fada wa magoya bayansa a wurin kamfen din cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci ta'addanci ba ko tada kayan baya, musamman daga yankin arewa maso gabas, New Telegraph ta rahoto.

Ya ce:

"Zan dawo da zama lafiya jihar saboda idan babu zaman lafiya, ba zai yiwu in cika dukkan alkawurran da na yi ba; Zan fatattaki Boko Haram. Boko Haram ba komai bane.
"Mun kawar da Boko Haram a Adamawa, mai zai hana mu fatattakarsu a Borno ko Yobe ko duk ina suke a kasar nan. Don haka ku zabe mu."

Abin Da Wike Ya Fada Wa Atiku A Sabuwar Ganawar Da Suka Yi Kan Rikicin PDP

Kara karanta wannan

Mun tuba: PDP ta tafka kura-kurai daga 1999 zuwa 2015, Atiku zai gyara komai

A kokarin warware rikicin jam'iyyar PDP, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya sake ganawa da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas.

Wata majiya da ta halarci taron ta shaidawa Daily Trust cewa wasu hadiminan bangarorin biyu sun halarci taron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164