Gwamna Ya Bayyana Yadda Takarar Peter Obi Za Ta Taimaki APC, Ta Gurgunta Atiku
- Gwamnan jihar Kano yana da ra’ayin cewa takarar da Peter Obi yake yi, zai taimaki APC ne a 2023
- Dr. Abdullahi Umar Ganduje yace ko a zaben 2019, APC ba ta samu kuri’u a Jihohin da ke kasar Ibo ba
- Ganduje yace Obi za iyi wa Atiku Abubakar illa ne, za su raba kuri’un da ake da su a Kudu maso gabas
Kano - A wata hira da aka yi da Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje a jiya, ya yi bayanin yadda siyasa take tafiya yayin da ake shirin zabe.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya shaidawa gidan talabijin Channels cewa jam’iyyar PDP ce ta shiga uku a dalilin fitowa takarar Peter Obi.
Mai girma Gwamnan yana ganin Obi da jam’iyyarsa ta LP za su yagi kuri’un da ya kamata a ce Atiku Abubakar ya samu ne a Kudancin Najeriya.
Abdullahi Umar Ganduje yace raba kuri’un da PDP da LP za su yi a jihohin Kudu maso gabashin Najeriya, shi zai taimakawa Bola Tinubu ya ci zabe.
Takarar Obi gaba ta kai mu inji Ganduje
The Cable tace Gwamnan yace dama can APC ba ta da karfi sosai a jihohin Ibo, saboda haka fitowar Peter Obi daga yankin zai gyara mata lissafi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ganduje yace APC mai mulki ba ta sa ran samun kuri’u da-dama daga yankin, don haka 'dan takaran PDP, Atiku Abubakar jam’iyyar LP za tayi wa illa.
"Ina tunanin fitowar Obi a matsayin ‘dan takaran jam’iyyar LP abin kirki ne ga jam’iyar APC domin PDP sune asalin abokan gwabzawarmu.
Wani karfi muke da shi a yankin Kudu maso gabas?
Kuri’un da muka samu a karamar hukumar Nasarawa a Kano, ya fi karfin duka abin da APC ta samu a jihohi biyar na Kudu maso gabas.
Saboda haka idan har aka samu wata matsala a tafiyar siyasa a Kudu maso gabashin Najeriya, jam’iyyar PDP ce za ta sha wahala sosai.
A dalilin wannan, ina tunanin fitowar Obi daga Kudu maso gabashin Kasar abu ne da zai tattara kuri’un da jam’iyyar PDP za ta samu."
- Gwamna Abdullahi Umar Ganduje
Atiku ba zai ci zabe ba - Kwankwaso
Da ya je Ribas domin bude ayyukan Gwamnatin Jihar, an ji labari Rabiu Musa Kwankwaso ya yabi Nyesom Wike a kan rikicin da ake yi da su.
Rabiu Kwankwaso yace babu ta yadda PDP za ta karbe shugabancin Najeriya a 2023 alhali ba ta da goyon baya sosai a jihohin Legas, Kano da Ribas
Asali: Legit.ng