Gwamnan PDP Wike Ya Yi Watsi da Atiku, Ya Zabi Kwakwaso a Matsayin Wanda Zai Yiwa Kamfen a Ribas
- Gwamnan jihar Ribas ya bayyana dan takarar shugaban kasa na biyu da zai taimakawa gabanin zaben 2023
- Ya ce ya zabi Kwankwaso ya yi gangami a jiharsa tare da taimakonsa saboda wasu halaye na kirki da yake dasu
- Wike ya yi irin wannan ga tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi yayin da ya ziyarci jiharsa a makon jiya
Jihar Ribas - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya yi alkawarin samar da kayayyakin da ake bukata na goyon baya ga dan takarar shugaban na jam'iyyar NNPP, Dr Rabiu Musa Kwankwaso.
Wike ya ce zai goyi bayan gangamin dan takarar na NNPP a jihar Ribas ta hanyar samar masa da dukkan kayayyakin da yake bukata na kamfen, Channels Tv ta ruwaito.
Wike ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da Kwankwaso ya kai ziyara Ribas don kaddamar da wasu ayyukan tituna da Wike ya yi a jihar.
Wike, wanda jigo ne na PDP ya gayyaci Kwankwaso domin kaddamar da ayyukan, inda ya siffanta dan takarar na NNPP da mai nagarta da Najeriya ke bukata.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce jihar Kano na da matukar muhimmanci ga nasarar PDP a zaben 2023, amma yana da kwarin gwiwa tare da fatan Kwankwaso ya kawo ta.
Na shawarci Kwankwaso kada ya bar PDP, amma kash!
Gwamnan ya kuma bayyana cewa, ya nemi Kwankwaso kada ya bar PDP a watan Maris, amma makiyan cikin gida a jam'iyyar suka tursasa shi barinta.
Wike ya ce Kwankwaso ne zai iya hada kan Najeriya wuri guda, amma kash, ba a jam'iyya daya suke a a yanzu.
Ba wannan ne karon farko da gwamna Wike ya bayyana goyon bayansa ga wani dan takarar da ba na jam'iyyar PDP ba.
Ga dai bidiyon lokacin da Wike ke jawabi:
Zan ba Petr Obi duk abin da yake bukata idan yazo kamfen jihar Ribas, inji gwamna Wike
A wani labarin, gwamna Wike ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, ya kuma ce zai bashi abin da yake so idan yazo kamfen jihar
Wike ya bayyana hakan ne bayan gayyato Peter Obi jiharsa domin kaddamar da ayyukan da ya yi a makon jiya
Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin jiga-jigan PDP da dan gwamnan PDP Wike.
Asali: Legit.ng