Bakar Wahala Na jiran 'Yan Najeriya a Gaba Idan Suka Ki Zaban Peter Obi, Inji Jigon Siyasa

Bakar Wahala Na jiran 'Yan Najeriya a Gaba Idan Suka Ki Zaban Peter Obi, Inji Jigon Siyasa

  • Wani jigon siyasa a kasar, Cif Charles Udeogaranya, ya nusar da 'yan Najeriya a kan babban abun da ke jiransu a gaba idan har suka yi zaben tumun dare a 2023
  • Udeogaranya ya yiwa al'ummar kasar albishir da shan bakar wahala da shiga kangin talauci idan har suka ki zaban Peter Obi na LP a matsayin shugaban kasa a zabe mai zuwa
  • Tsohon jigon na APC ya shawarci 'yan Najeriya da su kauracewa Bola Tinubu da Atiku Abubakar a 2023 idan har suna son kansu da arziki

Abuja - Cif Charles Udeogaranya wanda ya nemi takarar shugaban kasa a zaben 2019, ya shawarci 'yan Najeriya game da wanda ya kamata su zaba a matsayin wanda zai gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a babban zabe mai zuwa.

Udeogaranya ya gargadi ‘yan Najeriya a kan su shirya shan bakar wahala da tabarbarewar tattalin arziki idan suka ki zaban dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi a 2023, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Ku Yi Hattara Da Peter Obi, Kungiyar Matasan Kirista Ta Aike Da Sako Mai Karfi Ga Yan Najeriya

Peter Obi
Bakar Wahala Na jiran 'Yan Najeriya a Gaba Idan Suka Ki Zaban Peter Obi, Inji Jigon Siyasa Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Gargadin tsohon jigon na jam’iyyar APC na zuwa ne sa’o'i 74 bayan hukumar kididdiga ta kasa ta bayyana cewa ‘yan Najeriya miliyan 133 ne fama da talauci, lamarin da ya dare hasashen bankin duniya kan Najeriya.

A wani jawabi da ya saki a Abuja a ranar Lahadi, dan siyasar ya gargadi yan Najeriya masu zabe wadanda basa daukar batun zaban ingantaccen shugaba muhimmanci da su zauna su sake tunani game da bakar wahala da talaucin mutuwa da zai dabaibayekasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Idan yan Najeriya sun san abun da ya fi masu toh su kauracewa APC da PDP a 2023

Tsohon mai neman takarar shugaban kasar ya bukaci yan Najeriya da su kauracewa yan takarar shugaban kasa na jam’iyyun All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP).

A cewarsa duk kanwar j ace kuma yakamata mutanen da suka wuce lokacinsu su ba da damar da Najeriya zata rayu idan har suna nufin kasar da alkhairi.

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban Majalissar Dattijai Omo Ovie-Agege Yace Shine Ya Dakatar da Kudirin Tsige Shugaba Buhari

Dan siyasan ya kare zancewansa da cewa:

“Idan bamu wuce yan takarar shugaban kasa na APC da PDP ba, za su wuce da kaso 99.9 dinmu zuwa kangin talauci da bakar wahala.”

Muna bayan Peter Obi a 2023 don zagayen Inyamurai ne, Ohanaeze

Jaridar Punch ta rahoto cewa, a bangaren kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta ayyana goyon bayanta ga takarar shugabancin Peter Obi a zaben 2023.

A cewar babban kungiyar mai kare muradan Inyamurai yanzu zagayen kudu maso gabas ne ya samar da shugaban kasar Najeriya na gaba.

Peter Obi na neman kuri'un al'ummar yankin arewa, ya daukar masu babban alkawari

A wani labarin, Peter Obi ya yi alkawarin bunkasa harkar noma a yankin arewacin Najeriya idan har ya lashe zaben shugaban kasa a 2023.

Obi wanda ke zawarcin kuri'un mutanen yankin wanda nan ne ake zaton tushen talauci a kasar ya ce baya ga bunkasa noma, zai tabbatar da ganin farashin albarkatun gona sun kara daraja kafin fita da su kasashen waje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel