Obi Na Neman Kuri’un Yan Arewa, Ya Sha Alwashin Kawar Da Talauci

Obi Na Neman Kuri’un Yan Arewa, Ya Sha Alwashin Kawar Da Talauci

  • Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP ya daukarwa al'ummar arewa gagarumin alkawari muddin ya ci zabe a 2023
  • Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya ce zai fitar da yankin arewacin kasar daga kangin talauci wanda yayi masu katutu
  • Obi zai aiwatar da hakan ne ta hanyar mayar da hankali ga bangaren noma tare da daga darajar amfanin gonar kafin a fitar da su kasashen waje

Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Mista Peter Obi, ya fara zawarcin al'ummar yankin arewa, wanda ake zargin sune cibiyar talauci a kasar.

Obi wanda ke takara tare da Datti Baba-Ahmed ya daukin alkawarin cewa idan har aka zabe shi a 2023, gwamnatinsa za ta fitar da yankin daga kangin talauci, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Kungiyar Matan Zamfara Sun Ayyana Wanda Zasu Zaba Tsakanin Atiku da Tinubu a 2023

Peter Obi
Obi Na Neman Kuri’un Yan Arewa, Ya Sha Alwashin Kawar Da Talauci Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Kakakin kungiyar yakin neman zaben Obi-Datti, Dr. Yunusa Tanko, wanda ya yi magana a madadin ubangidansa, ya bayyana hakan ne a wani shirin kai tsaye Na gidan radiyon Bright FM Abuja, a ranar Asabar.

Tanko ya ce Obi wanda ya rike mukamin gwamnan jihar Anambra sau biyu, ya kudurci aniyar sauya labarin Najeriya zuwa mai kyau.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Obi zai bunkasa harkar noma a arewacin kasar

A cewarsa, dan takarar da tawagarsa masu kishin kasa sun fahimci tarin albarkatun da ke arewacin Najeriya musamman ma a bangaren noma don haka sun dauki aniyar mayar da hankali sosai kan noma don fitar da al’ummar yankin daga kangin talauci.

Tanko ya bayyana cewa ba a bangaren yin noma kadai Obi zai mayar da hankali ba harma da tabbatar da ganin amfanin gonar sun kara daraja kafin a fitar da su waje don samun abun da ake bukata don ci gaban kasar.

Kara karanta wannan

2023: Ku Yi Hattara Da Peter Obi, Kungiyar Matasan Kirista Ta Aike Da Sako Mai Karfi Ga Yan Najeriya

Matakin da LP zata dauka don tabbatar da ba a yi magudin zabe ba

Da yake magana game da shirye-shiryen LP don tabbatar da zabe mai inganci, ya yi bayanin cewa jam’iyyar ta fara daukar yan sa-kai.

A cewar Tanko, wadanan yan sa-kan za su yi aiki ba dare ba rana don tabbatar da ganin cewa an tura sakamakon yawan kuri’un da aka kada a kowace rumfa zuwa na’urar hukumar zabe kafin su bar wajen.

Ya ce ana iya zuba yan sa-kan da ya yiwa lakabi sojojin kurkuku a kowace rumfar zabe a fadin kasar kuma za su tsaya har sai an sanar da sakamako sannan an tura su zuwa na’urar INEC.

Obi: Zan fitar da yan Najeriya miliyan 130 daga talauci

Har ila yau, Peter Obi ya yi alkawarin fitar da yan Najeriya miliyan 130 daga talauci idan aka zabe shi a matsayin magajin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban Majalissar Dattijai Omo Ovie-Agege Yace Shine Ya Dakatar da Kudirin Tsige Shugaba Buhari

Obi ya bayyana hakan ne bayan ya halarci wani taro a Mkar, karamar hukumar Gboko ta jihar Benue, jaridar Daily Post ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng