Atiku Ya Yi Ganawar Sirri Da Jonathan, Mataki Na Yin Sulhu Da Wike
- Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya dauki matakin warware rikicin jam'iyyar a yayin da ya gana da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan
- Duk da cewa ba a san abin da aka tattauna a taron ba da aka yi a sirrance, an dade ana kira ga Atiku ya warware rikicin na PDP
- Akwai wani rahoto a baya da ya ce ana shirin kawo Jonathan domin ya warware rikicin yayin da tsohon shugaban kasar ya ce ba shi da hannu a rikicin da ke faruwa a jam'iyyar
Yenagoa, Bayelsa - Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ya yi ganawar sirri da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Duk da cewa ba a san abin da aka tattauna a taron ba, mai fatan zama shugaban kasar ya wallafa hotunan taron a sahihin shafinsa na Twitter a safiyar ranar Juma'a 18 ga watan Nuwamba.
2023: Ku Yi Hattara Da Peter Obi, Kungiyar Matasan Kirista Ta Aike Da Sako Mai Karfi Ga Yan Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da ke faruwa kan PDP, Atiku Abubakar, Ifeanyi Okowa, Goodluck Jonathan, Zaben 2023
Akwai wani tsegumi a baya da ke cewa Atiku da shugabannin PDP suna shirin tuntubar tsohon shugaban kasar don ya saka baki ya yi sulhu a rikicin da ke PDP.
Tun bayan da Atiku ya zama dan takarar shugaban kasa na PDP, jam'iyyar ta rika fama da rikice-rikice wanda har yanzu ba a yi sulhu ba.
Gwamnonin jihohin kudu a jam'iyyar na PDP karkashin jagorancin Nyesom Wike na jihar Rivers, suna kira da cewa shugaban jam'iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, ya yi murabus don adalci da daidaito.
Abin da ke faruwa kan rikicin PDP
Kuma, Ayo, ya bayyana cewa zai yi murabus daga mukaminsa idan har dan arewa ya zama dan takarar shugaban kasa kuma jam'iyyar ta bukaci hakan, amma kawo yanzu bai yi murabus din ba.
Rikicin na cigaba da wanzuwa a yayin da gwamnonin biyar da suke kiran kansu da G5 suka sha alwashin ba za su mara wa Atiku baya ba sai an biya musu bukatunsu.
2023: A Karshe Oshiomhole Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Tinubu Zai Kayar Da Atiku Domin Ya Ci Zaben Shugaban Kasa
A wani rahoton, Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa jam'iyyar All Progressives Congress, APC ne zai ci zabe.
Legit.ng ta rahoto cewa Kwamared Adams Oshiomhole, tsohon gwamnan jihar Edo ne ya yi wannan hasashen a ranar Juma'a 18 ga watan Nuwamba a Abuja.
Tsohon shugaban jam'iyyar ta APC na kasa ya ce kurakurai da dama da dan takarar shugaban kasar na PDP, Atiku Abubakar ya tafka za su bawa Tinubu damar yin nasara.
Asali: Legit.ng