Hukumar NAFDAC Tayi Sabuwar Mukaddashin Darakta Janar Ranar Alhamis

Hukumar NAFDAC Tayi Sabuwar Mukaddashin Darakta Janar Ranar Alhamis

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya nada sabuwar darakta janar ta hukumar kula da ingancin abinci da magunguna, NAFDAC, a yammacin Alhamis
  • Kamar yadda aka gano, Dakta Monica Eimunjeze ce ta samu darewa kujerar matsayinta ta babbar darakta hukumar
  • Majiyar da ta bukaci a boye sunanta ta sanar da cewa da yammacin Alhamis aka yi nadin kuma har yanzu bata hada taro da ma’aikatan ba

FCT, Abuja- Darakta a hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta NAFDAC, Dr Monica Elmunjeze, ta zama mukaddashin darakta janar ta hukumar.

Hukumar NAFDAC
Hukumar NAFDAC Tayi Sabuwar Mukaddashin Darakta Janar Ranar Alhamis. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Jaridar TheCable ta rahoto cewa, wannan yana zuwa ne bayan cikar wa’adin mulkin Farfesa Mojisola Adeyeye a matsayin darakta janar na hukumar.

Wani babban ma’aikaci a hukumar wanda ya bukaci a boye sunansa ya tabbatarwa da jaridar Punch hakan a ranar Alhamis da yammaci.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tsohon Ministan Noma Tsaro, Shettima Mustapha Ya Kwanta Dama

Majiyar tace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Babbar darakta ta hukumar, Monica, ita ce ta karba ragamar. Amma har yanzu bamu yi taro da ita ba saboda lamarin da yammacin nan ya faru.”

Duk kokarin da aka yi na jin ta bakin shugaban fannin yada labarai na hukumar, Sayo Akintola, a kan wannan cigaban ya gagara saboda baya daukar wayarsa ko martani kan sakon da aka tura masa a yayin rubuta rahoton nan.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Adeyeye matsayin darakta janar ta hukumar NAFDAC a ranar 3 ga watan Nuwamban 2017.

Mojisola Adeyeye, tsohuwar darakta janar ta hukumar ta tafi hutunta na ritaya.

An aikewa hukumar takardar nadin

A wata takardar cikin gida mai kwanan wata 17 ga Nuwamba wacce jaridar TheCable ta gani, Augustine Oboli, mataimakin darakta, yace hukumar ta samu wasikar nadin Eimunjeze matsayin mukaddashin darakta janar.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Amince da Tsige Shugaban NYSC Nan Take Kan Wani Muhimmin Abu

Oboli, wanda ya hada har da daraktoci 27 a wasikar, yace nadin Eimunjeze ya fara aiki a ranar 12 ga watan Nuwamba.

Gogewarta

Har zuwa nadinta, Eimunjeze ita ce daraktan rijista da daidaito ta hukumar.

Kafin nan, tayi aiki matsayin mataimakiya ga darakta janar din bincike da tantancewa ta kwayoyi.

Wacece Sabuwar daraktan?

Eimunjeze ta kammala karatu a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria da digito a fannin hada magunguna a 1986 kuma ta samu digirin digirgir a fannin hada magungunan daga jami’ar Mercer dake Georgia a Amurka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel