Shugaban Jam’iyya Yace Atiku da PDP Zasu Ci Zabe a Jihohi 24 – Har da Legas

Shugaban Jam’iyya Yace Atiku da PDP Zasu Ci Zabe a Jihohi 24 – Har da Legas

  • Shugaban jam’iyyar PDP a Najeriya ya karbi aikin da kwamitin Eyitayo Jegede ya yi a Legas da Osun
  • Eyitayo Jegede (SAN) aka ba nauyin sasanta sabanin da ke tsakanin ‘ya ‘yan jam’iyya a jihohin biyu
  • Iyorchia Ayu yana sa ran PDP ta karbe Legas da akalla jihohi 25 a zaben Gwamna da na Shugaban kasa

Abuja - Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr. Iyorchia Ayu yace za su doke APC mai mulki har a jihar Legas a zaben da za ayi a farkon shekara mai zuwa.

Leadership a rahoton da ta fitar a ranar Laraba, tace Iyorchia Ayu ya yi wannan bayani yayin da ya karbi rahoton aikin kwamitin Eyitayo Jegede (SAN).

Cif Eyitayo Jegede (SAN) shi ne ya jagoranci kwamitin yi wa ‘ya ‘yan PDP sulhu a Legas da Osun. Sulhun da aka yi ya karawa jam'iyyar kwarin gwiwa.

Kara karanta wannan

Jagora a Jam’iyyar LP Ya Dawo APC, Yace Peter Obi Ba Za Su Kai Labari a 2023 ba

Legas za ta koma hannun PDP

Shugaban jam’iyyar hamayyar yake cewa a baya PDP ba ta iya tabuka abin kirki a jihar Legas, yace a 2023 labari zai canza a dalilin aikin da Jegede ya yi.

Ayu yace jam’iyyar PDP za ta lashe zaben shugaban kasa, sannan kuma tayi nasara a akalla zaben gwamnonin jihohi 24, a ciki har da jihar 'dan takaran APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku Abubakar
'Dan takaran PDP, Atiku Abubakar Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Jihohi 25 da zaben shugaban kasa

"Shugabannin reshen jihar Legas sun ajiye duk wani bambancin da suke da shi a tsakaninsu, sun zo za a hadu tare domin ganin nasarar jam’iyya.
Muna addua da fatan sauran shugabanni a duka rassa za suyi aiki tare ta yadda zuwa farkon badi, PDP za tayi murnar samun Gwamnoni akalla 25.
Sannan mu yi babbar liyafa a fadar shugaban kasa, za mu cin ma wannan ne da irinku."

Kara karanta wannan

Jerin Gwamnonin PDP da Suka Gindaya Sharuda Kafin Su Goyi Bayan Atiku Abubakar

Aikin da muka yi - Eyitayo Jegede

Shi kuma Eyitayo Jegede, jaridar nan Vanguard ta rahoto shi yana yi wa jam’iyya godiya na musamman da aka ba shi damar zama jakadan dinke baraka.

Jegede yake cewa rahoton da suka gabatar sakamakon tattaunawa da suka yi da jiga-jigai, manya da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar adawar ne.

Jigon jam'iyyar yace a sanadiyyar aikinsu ne jam'iyyar ta ci zaben Gwamnan Osun.

Nadamar Suleiman Othman Hunkuyi

A matsayinsa na ‘Dan Adam, mun ji labari Suleiman Othman Hunkuyi yace goyon bayan jam’iyyar APC da ya yi a 2015 har aka doke PDP kuskure ya tafka.

Amma an ji Jam’iyyar APC tace Sanata Suleiman Othman Hunkuyi ya yi shekara da shekaru bai taba lashe zabe a jihar Kaduna ba, sai lokacin guguwar canji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng