Zaɓen 2023: Kunyata, Ɓacin Rai Yayin Da Magoya Bayan Suka Ƙi Bin Ɗan Takarar Gwamna Na APC Zuwa PDP

Zaɓen 2023: Kunyata, Ɓacin Rai Yayin Da Magoya Bayan Suka Ƙi Bin Ɗan Takarar Gwamna Na APC Zuwa PDP

  • Magoya bayan Mahmoud Maijama'a Ajiya, dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Bauchi sun juya masa baya bayan ya koma PDP
  • Magoya bayan, karkashin jagorancin Garba Musa Kore, sun ce sun dauki matakin ne saboda cigaba da jihar Bauchi
  • A cewar Kore, magoya bayan sun hada da mambobin majalisar dokokin jiha da tsaffin kwamishinoni a jihar

Bauchi, Bauchi - Magoya bayan dan takarar jam'iyyar gwamna na jam'iyyar All Progressives Congress, APC a jihar Bauchi, Mahmoud Maijama'a Ajiya, wanda a baya-bayan nan ya koma PDP sun juya masa baya.

Kwamitin gudanarwarsa, karkashin jagorancin ciyaman dinta, Garba Musa Kore, ya ce mambobinsa sun yanke shawarar ba za su bi shi zuwa PDP ba, Leadership ta rahoto.

Mahmoud Ajiya
Zaɓen 2023: Kunyata, Ɓacin Rai Yayin Da Magoya Bayan Suka Ƙi Bin Ɗan Takarar Gwamna Na APC Zuwa PDP. Hoto: PDP Updates.
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

A yi dai mu gani: Tinubu ya tara jama'a, ya yiwa Atiku da Peter tonon silili a Jos

Dan takarar gwamnan APC da ya koma PDP

Kore ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka yi a hedkwatar kungiyar yan jarida na Najeriya, NUJ, a Bauchi ranar 16 ga watan Nuwamba, rahoton Head Topics.

Ya kara da cewa an cimma matsayar ne a wani taro da aka yi a gidan Honarabul Hussaini Umar (Majikiran Bauchi) a ranar Lahadi, 13 ga watan Nuwamba a Bauchi.

Wani sashi na sanarwarsa ya ce:

"Mun cimma matsayar mu ne a taron da aka yi jiya, ranar 13 ga watan Nuwamban shekarar 2022 a gidan Honarabul Hussaini Umar (Majikiran Bauchi)."

Abin da ke faruwa a APC, PDP a Bauchi, Arewa, zaben 2023

A cewar Kore, kwamitin ta dauki wannan matakin ne saboda ganin hakan zai fi alheri ga mutanen jihar Bauchi.

Kwamitin ta kunshi mambobin majalisar dokoki na jihar da tsaffin kwamishinoni.

Sanatan APC, Adamu Bulkachuwa Ya Sauya Sheka, Ya Kama Tafiyar Atiku

Kara karanta wannan

Da Dumi: PDP Tayi Nasara Jam'iyyar APC Ba Tada Yan Takara a Kujerun Majalisar Rivers 16, Kotu ta Yanke hukunci

A bangare guda, kun ji cewa burin Tinubu na gadon kujerar Shugaba Buhari a zaben 2023 na ci gaba da gamuwa da cikas yayin da a kullum ake samun wadanda ke ayyana sauya sheka zuwa wasu jam'iyyu.

Sauya shekar wasu jiga-jigan APC a kwanakin nan na sake jefa alamar tambaya ga jam'iyyar tare da hango makomarta a zaben 2023.

A kokarin tafiyar 2023, wasu yan APC ba su ji a jikinsu jam'iyyar za ta tabuka wani abu ba, musamman duba da shugabancinta, yayin da wasu kuwa ke duba rikicin da ke cikin jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164