Tinubu Ya Yi Jimamin Rasuwar Dan Majalisar Dokokin Jihar Legas a Wurin Kamfe
- Bola Tinubu ya miƙa sakon ta'aziyyarsa ga iyalan ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Mushin II a majalisar dokokin jihar Legas
- Sobur Olawale, wanda aka fi sani da Omititi ya yanke jiki ya faɗi kuma rai ya yi halinsa jim kaɗan bayan kaddamar da kamfen APC a Jos
- Mai neman zama shugaban kasa a inuwar APC yace marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen cigaban Legas
Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan mamba a majalisar dokokin jihar Legas, Sobur Olawale, wanda ake kira da Omititi.
Olawale, shugaban kwamitin kananan hukumomi a majalisar Legas, ya yanki jiki ya faɗi kuma ya rasu jin kaɗan bayan kaddamar da fara kamfen shugaban ƙasa a Jos, babban birnin jihar Filato ranar Talata.
Rikicin PDP: Tsohon Shugaban APC Ya Dira Patakwal Yayin da Wike Ya Cigaba da Ɗasawa da Jiga-Jigan APC
Marigayi Olawale kafin rasuwarsa yana wakiltar mazaɓar Mushin ta II a majalisar dokokin jihar Legas.
Tsohon gwamnan ya miƙa sakon ta'aziyyar ne a wani rubutu da ya saki shafinsa na dandalin Tuwita ranar Laraba, 16 ga watan Nuwamba, 2022.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A sakon, Bola Tinubu yace:
"Ina miƙa ta'aziyyata ga iyalan Honorabul Sobur Olawale wanda har zuwa numfashinsa na ƙarshe da bamu yi tsammani ba jiya, shi ne mamba mai wakiltar mazaɓar Mushin II a majalisar dokokin jihar Legas."
"Omititi kamar yadda abokai da masoya ke kiransa a siyasance, ya kasance mutum mai son iyalinsa, mai sadaukarwa da yi wa jam'iyya biyayya, bai yi ƙasa a guiwa ba wajen goyon bayan haɓaka da cigaban Legas da Najeriya."
"Ina jajantawa iyalansa da ɗaukacin al'ummar mazaɓarsa kuma ina Addu'a Allah ya bai wa waɗanda ya bari hakurin jure rashinsa kuma Allah ya jikansa."
Yadda Ɗan majalisa ya rasa ransa a Jos
A wani labarin Mun kawo muku yadda Honorabul Sobur Olawale, yace ga garin ku nan wurin gangamin taron yaƙin neman zaɓen Tinubu a Jos
Bayanai sun nuna cewa Mamban majalisar dokokin ya yanki jiki ya faɗi ne tun a filin jirgin sama kuma duk wani kokari na ganin ya farfaɗo bai kai ga nasara, rai ya yi halinsa.
Tuni majalisar jihar Legas ta tabbatar da rasuwar mambanta, inda ta ayyana rashin mutum kamarsa da babbar asara ga al'umma.
Asali: Legit.ng