Keɓabbe: A Ƙarshe Tambuwal Ya Bayyana Alaƙarsa Da Ke Tsakaninsa Wike Bayan Zaben Fidda Gwani Na PDP

Keɓabbe: A Ƙarshe Tambuwal Ya Bayyana Alaƙarsa Da Ke Tsakaninsa Wike Bayan Zaben Fidda Gwani Na PDP

  • A yayin da ake cigaba da fama da rikici a jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, sabbin bayanai sun fito game da sulhu
  • Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya ce ana cigaba da tattaunawa don yin sulhu a jam'iyyar
  • Ya bayyana cewa jita-jitar da ake yadawa na cewa akwai matsala tsakaninsa da Wike ba gaskiya bane inda ya bayyana takwararsa na Ribas a matsayin aboki kuma dan uwa

FCT, Abuja - Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa babu wata matsala tsakaninsa da Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, Legit.ng ta rahoto.

Gwamna Tambuwal ya bayyana hakan ga wakilin jaridar Legit.ng na shiyya a Abuja wurin taron SDGs da aka yi a yayin taron tattalin arziki na Najeriya (NES28) karo na 28.

Kara karanta wannan

2023: Dan gwamna ya saba wa ra'ayin mahaifinsa kan dan takarar shugaban kasan wata jam'iyya

Wike da Tambuwal
A Ƙarshe Tambuwal Ya Bayyana Alaƙarsa Da Ke Tsakaninsa Wike. Hoto: Gov Nyesom Ezenwo Wike, Aminu Waziri Tambuwal.
Asali: Facebook

Babu rashin jituwa tsakani na da Wike - Tambuwal

Da aka masa tambaya kan cewa ko ya ga Gwamna Nyesom Wike tun bayan rikicin na PDP, sai ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Eh, muna haduwa, a kalla mun hadu kimanin wata daya da ta wuce."

Legit.ng ta sake yi masa tambaya idan akwai rashin jituwa tsakaninsu; Gwamna Tambuwal ya bada amsa yana cewa:

"Babu rashin jituwa tsakanin mu, abokina ne, dan uwa na ne."

Da ya ke magana kan rikicin na PDP, Gwamna Tambuwal ya bayyana cewa PDP ba yaki ta ke yi ba kuma duk abin da ke faruwa siyasa ne ba gaba ba.

Amma, ya bayyana cewa jam'iyyar ta PDP na aiki domin ganin ta warware rikicin cikin gidan saboda fuskantar babban zaben shekarar 2023.

Rikicin PDP: Ban Rufe Kofar Sulhu Ba, Atiku Ya Bawa Wike Amsa

Kara karanta wannan

Shugaban PDP Ya Bayyana Abin da Zai Jawo Atiku Ya Fadi Zaben Shugaban Kasa

A wani rahoton, dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, ya ce bai rufe kofa ba don yin sulhu da mutanen bangaren Gwamna Nyesom Wike, Daily Trust ta rahoto.

Bangaren na Wike sun fita daga kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Atiku ne kuma suka nemi Iyorchia Ayu ya yi murabus a matsayin shugaban jam'iyya na kasa saboda adalci da daidaito.

Amma, da ya ke magana a ranar Laraba a Bauchi, Wike, wanda shine jagoran gwamnonin da ke fushi da PDP, yayin ziyarar da suka kai wa takwararsu Bala Mohammed na jihar Bauchi ya ce har yanzu a shirye suke suyi sulhu da shugaban jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164