Kamfanin da Tinubu Yace Ya yi wa Aiki a kasar Waje Sun Ce Ba Su San Shi ba

Kamfanin da Tinubu Yace Ya yi wa Aiki a kasar Waje Sun Ce Ba Su San Shi ba

  • Bayanai da ke fitowa suna nuna Bola Ahmed Tinubu bai taba aiki da Deloitte a kasar Amurka ba
  • ‘Dan takaran shugaban kasar na APC ya taba cewa ya yi aiki da kamfanin, har ya samu kudi masu tsoka
  • Haka zalika ana tuhumar Tinubu da yi wa hukuma karya a lokacin da zai shiga zaben Gwamna a 1999

United States - Wata sabuwar takarda da ta fito daga kamfanin Deloitte a kasar Amurka, ya bayyana cewa Bola Ahmed Tinubu bai taba aiki da shi ba.

Rahoton da muka samu daga gidan talabijin na Arise TV ya nuna ba a taba yin lokacin da Bola Ahmed Tinubu yake aiki da kamfanin na Deloitte ba.

A baya, ‘dan takaran shugaban kasar ya yi ikirarin ya yi aiki da wannan kamfani mai binciken kudi.

Kara karanta wannan

Tonon Sililin da Gwamnan Anambra Ya Yi Wa Peter Obi Ya Tsokano Masa Fushin 'Obidients'

Da aka taba yin hira da shi a mujallar TheNews Magazine, tsohon gwamnan na Legas yace a kamfanonin Deloitte da Touche ya samu kudi a Amurka.

‘Dan siyasar yake cewa sai da ya tara Dala miliyan 1.8 daga albashi da kudin da ya samu daga kamfanonin kasar wajen, hakan ya zama silar arzikinsa.

An fara binciken kwa-kwaf

Wani ‘dan jarida mai binciken kwa-kwaf a Najeriya, David Hundeyin yace ya aika takarda zuwa ga kamfanin Deloitte USA domin suyi masa karin haske.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu
Shugaban kasa tare da Bola Tinubu a Jos Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Sakamakon binciken David Hundeyin kamar yadda ya wallafa a shafinsa na @DavidHundeyin a Twitter, shi ne akwai alamar tambaya a kan batun.

Rahoton yace ‘dan jaridar ya nuna jami’an Deloitte ba su da hujar da ke nuna sun yi aiki da Tinubu a baya. Hakan ya sake cusa 'dan takaran a cikin zargi.

Kara karanta wannan

Za a Iya Haramtawa Tinubu Shiga Takarar Shugaban Kasa Kwata-Kwata – Tsohon Jigon APC

Tinubu ya yi karatu a Ibadan?

Hundeyin bai gama bayaninsa ba sai ga Paul Ibe yana cewa akwai badakalar satifiket a tattare da ‘dan takaran shugaban kasar na jam’iyyar APC mai mulki.

Hadimin na Atiku Abubakar yace Tinubu ya yi wa hukumar INEC a 1999 karyar ya halarci jami’ar Chicago da makarantar sakandaren gwamnati ta Ibadan.

Gidan talabijin yace takardun da Ibe ya wallafa a shafinsa, sun yi kokarin nuna ‘dan takaran ya yi rantsuwar zur ne domin bai halarci makarantun nan ba.

Osinbajo ya ba Tinubu hakuri

Dazu aka ji labari Farfesa Yemi Osinbajo ya sha’afa yayin da yake jero sunayen manyan bakin da suka halarci jana’izar mahaifiyar Gwamnan Ondo.

Da aka nusar da shi, Mataimakin shugaban kasa ya ba Tinubu mai takarar shugabancin Najeriya hakuri, yace sam bai lura da shi a gefensa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng