Za a Iya Haramtawa Tinubu Shiga Takarar Shugaban Kasa Kwata-Kwata – Tsohon Jigon APC

Za a Iya Haramtawa Tinubu Shiga Takarar Shugaban Kasa Kwata-Kwata – Tsohon Jigon APC

  • Daniel Bwala ya yi sharhi a kan zargin da ake jifan Bola Ahmed Tinubu da shi na hannu a harkar kwayoyi
  • Mai magana da yawun bakin kwamitin takaran Atiku Abubakar yace ‘dan takaran yana da kalubale
  • Tsohon ‘dan jam’iyyar na APC mai mulki yace bai dace mutumin da ake zargi ya jagoranci al’umma ba

Abuja - Kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, Daniel Bwala yace akwai yiwuwar takarar Bola Ahmed Tinubu ta shiga matsala.

A ranar Alhamis, 10 ga watan Nuwamba 2022, Daniel Bwala yace za a iya hana ‘dan takaran na APC tsayawa a zaben shugaban kasa da za ayi a 2023.

‘Dan siyasar ya yi wannan magana a lokacin da aka yi hira da shi a shirin siyasar tashar Channels.

Bwala wanda yake magana da yawun kwamitin takaran Alhaji Atiku Abubakar, yace zargin da ake yi wa Tinubu na harkar kwayoyi zai kawo cikas.

Kara karanta wannan

2023: Tun da ‘Dan takaransa ya sha kashi, Buratai ya nuna wanda yake goyon baya

“Ina tsoron cewa a karshe ta fuskar shari’a…za a iya hana Bola Tinubu shiga takara idan har maganar ta je gaban Alkali.
Harka da safarar miyagun kwayoyi ko a Najeriya ko a kasar Amurka ne, babban laifi ne.”

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

- Daniel Bwala

Asiwaju Tinubu
Asiwaju Tinubu Hoto: officialasiwajubat
Asali: Facebook

Rahoto yace Bwala yana sharhi ne a kan takardun da wata kotu da ke Arewacin jihar Illinois a kasar Amurka ta fitar a game da ‘dan siyasar Najeriyan.

Ana zargin Tinubu ya shiga harkar kwayoyi shekaru 30 da suka wuce. Sau da-dama APC, PCC da magoaya bayan 'dan siyasar sun karyata wannan.

Shugaba bai da gaskiya?

Lauyan yace lamarin nanya taba martabar tsohon gwamnan na Legas da ake jifa da zargi, yace bai dace wanda ake tuhuma da laifi ya zama shugaba ba.

“A wajen mutanen Najeriya, silar kudi yana da muhimmanci, amma har yanzu akwai zargin harkar kwaya a kan wuyan mai neman zama shugaban al’umma.

Kara karanta wannan

Alkawari kaya: Tinubu ya fadi yadda zai yi da 'yan IPOB idan ya gaji Buhari a 2023

A ‘yan kwanakin nan an yi ta bankado hodar iblis a Najeriya, ana harkar kwayoyi a duk Duniya.
Idan aka zabi mutum mai kashi a jikinsa ya zama shugaban kasa, hakan na nufin zai taimakawa masu harkar nan, shiyasa ake neman mara kashi a gindi.

- Daniel Bwala

Za mu bi Tinubu a 2023 - 'Yan Arewa

An ji labari Jagororin yi wa Asiwaju Bola Tinubu kamfe a Arewa sun ce za su mara masa baya a zabe mai zuwa, amma sun gindaya sharadin da za a cika.

Kwamitin yakin neman zaben APC a zaben shugaban kasa yace zai hana Rabiu Kwankwaso yin tasiri a yankin da ya fito watau Arewa maso yamma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel