Tsohon Gwamna Kwankwaso Ya Fallasa Asirin Gwamnoni na Satar Dukiyar Talakawa
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yace Gwamnoni na satar dukiyar al’umma da sunan kudin inganta tsaro
- ‘Dan takaran Shugaban kasar yayi ikirarin bai taba karbar wadannan kudi har ya gama mulki a Kano ba
- Kwankwaso yace zai soke tsarin cin kudin tsaro da zarar ya zama shugaban Najeriya a inuwar NNPP
Abuja - Rabiu Musa Kwankwaso mai takarar shugabancin Najeriya ya halarci wani zama da aka yi da mutane domin bayyana masu manufofinsa a Abuja.
A wannan tattaunawa da Channels TV ta shirya a ranar Lahadi, Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi gwamnonin jihohi da karkatar da dukiyar jihohi.
Legit.ng Hausa ta saurari wannan zaman, inda ‘Dan takaran shugaban kasar yace gwamnoni su kan wawuri kudin jama’ansu ta karkashin kasafin tsaro.
Kwankwaso mai neman shugabanci a karkashin jam’iyyar hamayya ta NNPP yace a lokacin da yake gwamna a Kano, bai taba karbar wadannan kudi ba.
Kamar yadda The Nation ta fitar da rahoto, ‘dan siyasar ya yi alkawarin idan har mulkin Najeriya ya shigo hannunsa, zai dakatar da salon satar a jihohi.
Kwankwaso wanda ya yi gwamna a jihar Kano sau biyu tsakanin 1999 da 2015 yace kudin tsaro da ake ba jihohi bai taimakawa talakawan da ake mulka.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An rahoto shi yana cewa da zai samu shugabanci, zai soke wannan tsari a gwamnatance.
Abin da Kwankwaso ya fada
"A tsawon shekaru takwas da nayi ina Gwamnan jiha, ban taba cin ko sisi a cikin kudin tsaro ba, duk da na gaji gwamnatin da tayi imani da wannan.
Abin da nayi shi ne na saurari kalubalen rashin tsaro daga bakin Kwamishinan ‘yan sanda, sai na kai maganar zuwa majalisar domin a tattauna a kai.
A ra’ayina kudin tsaro babbar hanya ce ta satar dukiyar, shiyasa ban karba ba da ina gwamna. Idan na karbi mulki, babu kudin tsaro ga shugaban kasa."
- Rabiu Musa Kwankwaso
Neman kudin kamfe
A yau ne Buba Galadima ya fada mana duk dukiyar da Bola Tinubu ko Atiku Abubakar suke takama da ita, kudin sata ne da ake shirin sayen kuri’u.
Sanin kowa ne a Najeriya neman takarar shugaban kasa sai da kudi, Injiniya Buba Galadima yace dukiyar da NNPP ta tara shi ne dinbin mutanen da ta gina.
Asali: Legit.ng