Yadda APC, PDP, LP da NNPP Suke Shirin Tara Biliyoyin Kudin Yakin Neman Zabe
- Bayanai suna fitowa kan yadda jam’iyyun siyasa za su tanadi kudin yakin neman zabe a shekarar 2023
- Shiga takarar shugaban kasa tana bukatar kudi, don haka ne ‘yan takara ke neman makudan biliyoyi
- Jam’iyyu sun nuna shirin da suke yi, Buba Galadima yace NNPP ba ta bukatar kudi wajen cin zabe
Abuja - Punch tace Gwamnonin jihohi 22 da jam’iyyar APC take da su, za su taimaka sosai wajen tarawa Asiwaju Bola Tinubu kudin da zai yi yakin zabe.
Darektan yada labarai da hulda da manema labarai a kwamitin neman zaben APC, Bayo Onanuga ya karyata zargin cewa da kudin sata za suyi kamfe.
Onanuga yace gwamnoni, manyan 'yan majalisa da jagororin kamfe za su nemawa jam’iyya kudi a karkashin jagorancin wasu tsofaffin Gwamnoni hudu.
Kakakin kwamitin yakin neman zaben yace duka Gwamnonin APC 22 suna tare da Bola Tinubu. Onanuga yace yawan gwamnoninsu zai taimake su sosai
Wani hali PDP take ciki?
A gefe guda kuma, rahoton yace kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP, ya zargi Gwamnonin jam’iyya da tsuke bakin aljihu, sun ki sakin kudi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Timothy Osadolor yace maganar cewa Atiku Abubakar yana jiran wasu su taimaka masa da kudi ba gaskiya ba ne, domin ‘dan takaran na PDP a shirya yake.
Osadolor yace Atiku Abubakar ba ya kukan karancin kudi, amma duk da haka wannan ba zai sa ya ki karbar gudumuwa idan masoyansa sun kawo ba.
Kakakin kwamitin neman zaben shugaban kas ana PDP, Charles Aniagwu yace daidaikun mutane, kungiyoyi da masu ruwa da tsaki na ta kawo gudumuwa.
Jama'a za su taimaka mana - LP
Ita kuwa jam’iyyar LP tace za ta dogara ne da gudumuwar da magoya baya da masoya a Najeriya za su bada domin ayi nasara a yakin neman takaran badi.
Jaridar ta rahoto LP tana cewa ba za ta kashe kudi masu yawa wajen kamfe ba. A halin yanzu jam’iyyar hamayyar ta LP ba ta da Gwamna ko daya mai-ci.
Buba Galadima: Mu kuwa ke da kudi
Buba Galadima wanda yana cikin jiga-jigan NNPP ya shaidawa Legit.ng Hausa cewa su ne suke da kudi domin sun kafa dubunnan matasa a fadin Najeriya.
Injiniya Galadima yace akwai matasa a jihohi dabam-dabam da Rabiu Kwankwaso ya yi sanadiyyar suka zama mutane, da yanzu suke taimakawa NNPP.
Baban ‘Dan siyasar yace manyan jam’iyyun nan sun samu dukiya ne ta hanyar sata, kuma bai kamata talaka ya bari a saye shi da kudinsa da aka sace ba.
Har jam’iyyar APGA ta bakin ‘dan takaranta, Peter Umeadi tace ba ta fama da karancin kudi, kuma ta shiryawa yakin neman zaben shugaban kasa.
Shari'a da Tinubu a kotu
A makon jiya aka labari Alkalin kotun tarayya na Abuja ya amince da wasu bukatun Lauyan wata kungiya da ta kai karar Bola Tinubu, APC da kuma INEC.
Kungiyar mai zaman kanta, ta na so a matsawa Hukumar INEC lamba domin ta cire ‘Dan takaran APC, Tinubu daga cikin masu neman shugabancin Kasa.
Asali: Legit.ng