Mambobin PDP Sama da 12 Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Ƙaduna, Uba Sani Ya Magantu

Mambobin PDP Sama da 12 Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Ƙaduna, Uba Sani Ya Magantu

  • Mai neman zama gwamnan Kaduna a inuwar APC, Uba Sani, ya karɓi tuban mambobin PDP sama da 12,000 a Giwa
  • Uba Sani, Sanatan Kaduna ta tsakiya yace jam'iyyar PDP ta mutu murus a ƙaramar hukumar Giwa tun kafin zuwan 2023
  • Ya roki al'ummar yankin da su zaɓi 'yan takarar APC tun daga sama har ƙasa a zaɓe mai zuwa

Kaduna - Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Uba Sani, yace a kullun mambobin jam'iyyar PDP a jihar ƙara raguwa suke yayin da suke sauya sheka zuwa APC gabanin babban zaɓen 2023.

Sanata Uba Sani, wanda ke takarar gwamnan Kaduna karkashin inuwar APC, ya ƙara da cewa jam'iyyar adawa ta mutu murus a ƙaramar hukumar Giwa.

APC a Giwa, Kaduna.
Mambobin PDP Sama da 12 Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Ƙaduna, Uba Sani Ya Magantu Hoto: The Deputy Governor Of Kaduna State
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Uba Sani ya yi wannan furucin ne a Giwa lokacin da ya karɓi masu sauya sheka 12,817 daga PDP zuwa APC ranar Lahadin nan.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Samu Gagarumin Goyon Baya, Dubbannin Kusoshin APC da LP Sun Koma PDP a Jihar Arewa

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa daga cikin jiga-jigan PDP da suka sauya shekar har da tsohon kwamishina, shugabannin mata da kuma na matasa a sassan ƙaramar hukumar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan takarar gwamna na APC ya tabbatarwa masu sauya shekan cewa ba za'a nuna musu banbanci ba domin yanzun sun zama ɗaya da kowa.

"A jam'iyyar APC bamu nuna banbanci, waɗanda suka shigo yau ɗaya suke da mutanen da suka kafa jam'iyyar. Ɗaya muke kuma kan mu a haɗe yake," inji shi.

Ku zaɓi APC Sak a zaɓen 2023 inji Uba Sani

Sanata Sani ya buƙaci mazauna yankin Giwa su tabbata sun kaɗa wa 'yan takarar APC a babban zaben 2023 tun daga sama har ƙasa.

"Ku zaɓi Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa, Muhammad Sani Dattijo a matsayin Sanatan Kaduna ta tsakiya, Jibril Zubairu a matsayin mamba mai wakiltar Giwa/Birnin Gwari a majalisar wakilai."

Kara karanta wannan

Attahiru Jega Da Baba-Ahmed Sun Faɗi Sunan Ɗan Takarar Da Ya Dace 'Yan Najeriya Su Zaba a 2023

"Sannan ku zaɓe ni a matsayin gwamnanku da kuma Umar Auwal Bijimi da Adamu Mohammed Shika a matsayin mambobin da zasu wakilci mazaɓun Birnin Gwari ta yamma da Gabas majalisa jiha."

Wani mamban APC a karamar hukumar Kaduna ta kudu, Zaharadden Nura, ya shaida wa wakilin Legit.ng Hausa cewa jam'iyya mai mulki na da shirye-shiryenta a ƙasa da zasu kaita ga nasara.

Yace idan ka duba yadda mutane ke tururwar shiga APC zaka iya nazarin cewa akwai wasu kulle-kulle da take kuma ba haka bane, siyasa ce kawai.

"Mu a APC ta kaduna sai dai muce Alhamdulillahi, muna aiki tukuru kuma muna kokarin jawo hankalin mata domin yanzun suke da yawan kuri'u, tun daga fari zamu jawo su APC, inada yakinin Tinubu da Uba Sani zasu ci zaɓe."

Legit.ng Hausa ta kuma zanta da wani mazaunin Giwa, wanda ya halarci taron sauya shekar don gane wa idonsa amma ya nemi a boye bayanansa saboda wasu dalilai na ƙashin kai.

Kara karanta wannan

Ta Kare Wa Atiku, Tsohon Shugaban PDP, Jiga-Jigai da Mambobi Sama da 40,000 Sun Koma APC a Arewa

Ya faɗa wa wakilinmu cewa, "Mutanen da na gani ba su wuce 500 ba, idan sun fi haka ba zasu zarce 1000 ba. Inda aka ware wa masu suaya shekar na hangi wasu fulani ne."

Bugu da kari, yace a halin yanzun mutane jira suke ranar zaɓe ta yi su zaɓi wanda suke so, ya yi Addu'ar Allah ya ba ƙasar nan shugabanni nagari.

A wani labarin kuma Jam'iyya mai kayan marmari NNPP ta samu karin goyon bayan a jihar Gombe yayin da mambobin APC da PDP suka koma inuwarta

Bayanai sun nuna cewa ɗan takarar gwamnan Gombe a jam'iyyar NNPP, Khamisu Mailantarki ne ya karɓi dandazon masu sauya shekar tare da wasu kusoshi.

A jawabinsa, yace matakin da suka ɗauka ba karamar nasara bace kana ya tabbatar musu da cewa ba za'a nuna musu wariya wurin tafiyar da harkokin siyasa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262