Attahiru Jega da Baba Ahmed Sun Ayyana Dan Takarar Da Ya Dace Mutane Su Zaba a 2023

Attahiru Jega da Baba Ahmed Sun Ayyana Dan Takarar Da Ya Dace Mutane Su Zaba a 2023

  • Tsohon shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega, da kakakin dattawan Arewa sun bi bayan ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PRP
  • Jega yace ɗan takarar PRP ya haɗa duk wata nagarta da kwarin guiwa lashe zaɓen shugaban kasa da kafa gwamnati a 2023
  • Hakeem Baba-Ahmed, ya bi sahun Jega, ya ayyana goyon baya ga Kola Abiola, ya gaji shugaban kasa Buhari

Abuja - Tsohon shugaban hukumar zaɓe INEC, Farfesa Attahiru Jega, da kakakin ƙungiyar dattawan arewa, Hakeem Baba-Ahmed, sun zaɓi ɗan takarar da suke ganin ya dace da Najeriya a 2023.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Jega da Baba-Ahmed sun ayyana goyon bayansu ga ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PRP, Kola Abiola, domin taimaka masa ya lashe zaɓen 2023.

Dan takarar PRP, Kola Abiola.
Attahiru Jega da Baba Ahmed Sun Ayyana Dan Takarar Da Ya Dace Mutane Su Zaba a 2023 Hoto: punchng
Asali: UGC

Farfesa Jega da Hakeem Baba-Ahmed sun ayyana matsayarsu ne a wurin taron kaddamar da manufofin PRP da ya gudana a birnin tarayya Abuja ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Gwamnan Arewa Ya Rantsar da Shugaban Ma'aikata Da Sabbin Ciyamomi 17 a Jiharsa

Da yake ayyana goyon bayansa a wurin taron, Jega ya yi shaguɓe ga masu yamaɗiɗin cewa zaben shugaban kasa na 2023 tseren zakuna uku ne kaɗai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yace, "Ba abin mamaki bane mutane na ta faɗin kalamai yadda ransu ke so, wasu abun dariya ma. Wata karin magana na cewa, 'Ba'a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare"

"Ina mai faɗa muku cewa ɗan takararmu, Kola Abiola, ya shirya tsaf kuma yana da manufa, mutum ne na daban wanda idan aka yi la'akari da kwarewarsa ya yi wa sauran 'yan takara fintinkau."

Tsohon shugaban INEC wanda ya nuna mamba ne mai alfahari da PRP, ya ƙara da cewa jam'iyyarsa ce ta fi dacewa ta karɓi mulki domin ceto ƙasar nan, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Baba-Hakeem ya bi sahun Jega

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC Ta Lallasa Jam'iyyu 12, Ta Lashe Zaben Ciyamomi 25 a Jihar Arewa

A nasa jawabin, mai magana da yawan NEF, Hakeem Baba-Ahmed, ya bi sahun Jega wurin ayyana goyon bayansa ga ɗan marigayi Abiola, fitaccen ɗan kasuwa.

Yace ɗan takarar na da kwarin guiwa da kwarewar da zai ja ragamar jam'iyyar PRP zuwa fadar shugaban ƙasa a 2023.

Baba-Ahmed ya kuma bukaci mambobin jam'iyya da sauran 'yan takara su yi aiki tuƙuru don tabbatar da sun lashe kowace kujerar siyasa a babban zaɓen dake tafe a shekara mai zuwa.

"Mun rungumi PRP ne saboda mun san zata iya lashe zaɓen shugaban kasa kuma ta kafa gwamnati. Muna da mutane da dabaru kuma munsan sauran yan adawa ba su kaimu ba."

A wani labarin kuma Sanata Dino Melaye ya yi ikirarin cewa wasu gwamnonin PDP dake tsagin Wike zasu dawo bayan Atiku gabanin 2023

Mai magana da yawun kwamitin kamfen shigaban kasa na PDP yace Wike ne ya kawo shugaban PDP na ƙasa, Ortom ya tsaya masa.

Kara karanta wannan

Awanni Gabanin Fara Wa, Jam'iyyar PDP Ta Tsame Kanta Daga Zaben Kananan Hukumomi a Jihar Arewa

Yace yana mamakin yadda suke yaƙar mutumin da sune suka kafa shi a kujerar, yace nan gaba wasu zasu dawo daga rakiyar Wike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel